Jam'iyyar APC Ta Dage Babban Taro Na Ƙasa Har Sai Baba Ta Gani

Jam'iyyar APC Ta Dage Babban Taro Na Ƙasa Har Sai Baba Ta Gani

  • Jam'iyyar APC ta ɗage babban taron masu riƙe da muƙamai da taron majalisar zartarwa (NEC) wanda aka shirya gudanarwa Talata da Laraba
  • Ta ce zata sanar da sabbin ranakun da za a gudanar da manyan tarukan nan gaba kaɗan bayan an cimma matsaya
  • APC ta kuma tabbatar da cewa Abdullahi Adamu ya yi murabus daga muƙaminsa yayin da Sakataren jam'iyya ya take masa baya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Kwamitin gudanarwa na APC ta ƙasa (NWC) ya ɗage babban taron masu ruwa da tsaki da taron majalisar kolin jam'iyyar (NEC) har sai baba ta gani.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa wannan mataki na zuwa ne bayan Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus daga matsayin shugaban APC ta ƙasa.

Mukaddashin shugaban APC na ƙasa, Abubakar Kyari.
Jam'iyyar APC Ta Dage Babban Taro Na Ƙasa Har Sai Baba Ta Gani Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Tun da fari an tsara gudanar da tarukan a ranakun 10 da 11 ga watan Yulin da muke ciki amma aka ɗaga zuwa gobe Talata da washe garin Laraba.

Kara karanta wannan

APC Ta Tabbatar da Cewa Shugaba da Sakataren Jam'iyya Sun Yi Murabus, Ta Maye Gurbinsu

Da yake zanta wa da yan jarida a ƙarshen taron NWC na gaggawa da ya gudana a Abuja, mukaddashin shugaban APC, Sanata Abubakar Kyari, ya ce sun ƙara ɗaga taron.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Duba da abinda ya faru, muna sanar da cewa an ɗage taron masu ruwa da tsakin APC da majalisar zartarwa (NEC) wanda a baya aka tsara gudanarwa ranar 18 da 19 ga watan Yuli."
"Ba zamu ce ɗagawar sai baba ta gani ba, nan gaba kaɗan zamu sanar da sabbin ranakun gudanar da muhimmin taron."

- Abubakar Kyari.

Sakataren APC na ƙasa ya yi murabus daga muƙaminsa

A jawabinsa, sabon shugaban APC mai mulki, Sanata Kyari ya tabbatar da cewa sakataren jam'iyyar, Mista Iyiola Omisore ya yi murabus daga kujerarsa.

Ya kuma bayyana cewa tuni shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya sauka daga kujerarsa kuma ya maye gurbinsa a taron NWC da ya gudana a Abuja ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Samu Babbar Matsala a Wurin Taron APC Na Ƙasa, Sakatare Ya Fice Daga Wurin

Wannan ya kawo karshen raɗe-raɗin da ake ta yaɗa wa cewa Adamu ya yi murabus, ya tura takarda ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

APC ta maye gurbin sakatare na ƙasa

Vanguard ta ce kwamitin gudanarwa (NWC) ya bayyana cewa mataimakin sakataren APC, Barista Festus Fuanter, ya maye gurbin Omisore a matsayin muƙaddashin sakatare.

Sanata Omisore Ya Fice Daga Wurin Taron Gaggawa Na APC

A wani rahoton Sakataren jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Iyiola Omisore, ya fice daga wurin taron gaggawa na kwamitin gudanarwa (NWC).

Jim kaɗan bayan isa wurin, aka ga sakataren APC na ƙasa, Sanata Omisore ya shiga mota ya bar sakatariyar ba tare da ya yi hira da 'yan jarida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262