Tinubu: Jerin Yan Siyasar Da Suka Zama Gwamnoni a Ganiyar Shekarunsu Ta 30s a 1999

Tinubu: Jerin Yan Siyasar Da Suka Zama Gwamnoni a Ganiyar Shekarunsu Ta 30s a 1999

Shugaban kasa Bola Tinubu na daya daga cikin yan siyasa masu sa'a da suka zama gwamna a 1999, shekarar da Najerita ta koma mulkin damokradiyya bayan shekaru 16 na mulkin soji.

Da yawansu, gwamnonin rukunin 1999 sun ziyarci shugaban kasa Tinubu a fadar shugaban kasa a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli, lamarin da ya yi kama da haduwar zumunci ga tsoffin gwamnonin.

Gwamnonin da aka zaba tare da Tinubu a 1999
Tinubu: Jerin Yan Siyasar Da Suka Zama Gwamnoni a Ganiyar Shekarunsu Ta 30s a 1999 Hoo: Bola Ahmed Tinubu, Chimaroke Nnamani
Asali: Twitter

Abun da tsoffin gwamnonin suka fada wa Shugaban kasa Bola Tinubu

Tsoffin gwamnonin sun ziyarci fadar shugaban kasa don taya takwaransu, wanda ya yi aiki a matsayin gwamnan jihar Lagas tsakanin 1999 da 2007 murna. Sun nuna goyon bayansu ga manufofin shugaban kasa Tinubu tun bayan da ya kama mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Abun ban sha'awa, uku daga cikinsu sun zama gwamnonin jihohinsu lokacin da suke matasa yan kasa da shekaru 40. Dukkansu an zabe su ne a karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), kuma har yanzu ana damawa da su a siyasa.

Kara karanta wannan

Jerin Takwarorin Shugaban Kasa Bola Tinubu Na 1999 10 Da Suka Mutu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An lissafa gwamnonin a kasa:

Chimaroke Nnamani

Nnamani, wanda aka haifa a ranar 30 ga watan Mayun 1960, ya kasance gwamnan jihar Enugu sau biyu tsakahin 1999 da 2007.

An rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Enugu yana da shekaru 38 sannan ya kammala wa'adinsa na biyu a matsayin gwamna yana da shekaru 46.

Orji Uzor Kalu

Kalu, wanda aka haifa a ranar 21 ga watan Afrilun 1960 ya zama gwamnan jihar Abia da dawowar damokradiyya kasar a 1999 kuma ya shafe wa'adi biyu.

Sanatan ya kama mulki a matsayin gwamnan jihar Abia yana da shekaru 39 sannan ya kammala yana da shekaru 47.

James Ibori

Tsohon gwamnan na jihar Delta na daga cikin masu sa'a da suka hau karagar mulki a 1999 a lokacin da yake shirin cika shekaru 40.

Kara karanta wannan

Yadda Bincike da Zargin Sata Zai Jawo Na Hannun Daman Tinubu Su Rasa Ministoci

An rantsar da Ibori a ranar 29 ga watan Mayu a matsayin gwamnan jihar Delta lokacin da yake da shekaru 39 kuma yan watanni kafin bikin cikarsa shekaru 40. An haife shi a ranar 4 ga watan Agustan 1959.

Yar'Adua, Alamieyeseigha, da wasu gwamnonin 1999 da suka mutu

A gefe guda, mun ji cewa akalla 10 daga cikin gwamnonin rukunin 1999 ne suka kwanta dama a cikin shekarun bayan zabensu na 1999.

Yar'Adua, Alamieyeseigha, Kachalla na daga cikin tsoffin gwamnonin da suka rasu cikin shekarun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: