Shaidan PDP Ya Rikice, Ya Gaza Tabbatar da Ikirarin Shi Wakilin Akwatu Ne a Kotu

Shaidan PDP Ya Rikice, Ya Gaza Tabbatar da Ikirarin Shi Wakilin Akwatu Ne a Kotu

  • An yi wata yar dirama a Kotun sauraron ƙarar zaben gwamnan Ogun mai zama a Abeokuta ranar Jumu'a
  • Lamarin ya faru ne yayin da PDP ta gabatar da shaida, Isah Lawal, wanda daga ƙarshe ya riƙa tufka da warwara a bayanansa
  • Zaman dai bai yi wa jam'iyyar PDP daɗi ba a kokarinta na ganin ta kwace nasarar da gwamna Dapo Abiodun na APC ya samu a zaben 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ogun - An yi wata yar ƙaramar dirama a Kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamna mai zama Abeokuta, babban birnin jihar Ogun yayin zaman ranar Jumu'a 14 ga watan Yuli.

Vanguard ta rahoto cewa lamarin ya faru ne yayin da jam'iyyar PDP ta kira ɗaya daga cikin shaidunta mai suna, Isah Lawan, wanda ya yi ikirarin shi wakilin akwatu ne.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Jam'iyyar APC Ta Yi Magana Kan Gwamnanta Mara Lafiya, Ta Bayyana Lokacin Da Zai Dawo Najeriya

Shaidar PDP ya ruɗe a gaban Kotun zabe a Ogun.
Shaidan PDP Ya Rikice, Ya Gaza Tabbatar da Ikirarin Shi Wakilin Akwatu Ne a Kotu Hoto: PDPNigeria
Asali: UGC

Mista Lawal ya bai wa jam'iyyar PDP kunya yayin da ya gaza tsayuwa kan ikirarinsa na farko cewa shi wakilin jam'iyyar ne a rumfar zaɓe lokacin zaɓen gwamna ranar 18 ga watan Maris.

Lawal ya gabatar da kansa a Kotu da cewa shi mazaunin Makun a yankin Sagamu ne kuma ya yi aiki a matsayin wakilin PDP a rumafar zaɓe mai lamba PU002, Ward 12.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma lokacin da lauyan APC ya faɗa masa cewa akwai wani mai suna Yewande Babatunde, shi ne Ajent ɗin PDP a wannan rumfar zaɓe, nan take shaidan ya saɓa ikirarinsa.

Abu kamar wasan kwaikwaiyo, sai aka ji mutumin da bakinsa yana cewa ya san Yewande Babatunde kuma zancen gaskiya shi ne wakilin PDP a wannan rumfar zaɓe.

Shaidan ya kunyata PDP kuma asirinsa ya tonu yayin da ya gaza gamsar da Kotu da kwararan shaidu cewa ya yi aiki a matsayin Ajent din PDP a akwatun 002 ranar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Matawalle Ya Gabatar da Kwararan Shaidu 19 Domin Tsige Gwamna Dauda Lawal Na Zamfara

Yadda zaman Kotun ya kaya

Tun da fari, a zaman ranar Jumu'a, lauyan hukumar zaɓe INEC ya ankarar da Kotu cewa akwai kamanceceniya a bayanan shaidu daban-daban da PDP ta gabatar kuma suna saɓa wa juna.

Sai dai nan take lauyan PDP, Goddy Uche, ya nuna jayayya amma kwamitin Alkalan Kotun ya yi watsi da ƙorafinsa, ya ɗauki ankararwan lauyan INEC, News Hedlines ta ruwaito.

Cire Tallafi: Gwamna Nwifuru Ya Kara Wa Ma'aikata Albashi a Jihar Ebonyi

A wani labarin kuma Gwamna Francis Nwifuru ya ƙara wa ma'aikatar jihar Ebonyi albashin domin rage masu raɗaɗin cire tallafin mai.

Gwamnan ya aminta da ƙara ɗaukar sabbin ma'aikata 1,454 a faɗin kananan hukumomin jihar da ke shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262