Zulum Ya Nada Barkindo Saidu a Matsayin Daraktan Hukumar Ba Da Agaji Ta Jihar Borno

Zulum Ya Nada Barkindo Saidu a Matsayin Daraktan Hukumar Ba Da Agaji Ta Jihar Borno

  • Farfesa Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya sanar da nadin Barkindo Saidu a matsayin shugaban hukumar SEMA ta jihar Borno
  • Haka nan Gwamna Zulum ya kuma sanar da nadin Abdulkadir Haruna, a matsayin shugaban hukumar ilimin larabci da tsangayu ta jihar (BOSASEB)
  • Sanarwar nade-naden ta fito ne daga wajen mai bai wa Zulum shawara kan harkokin yada labarai, Isa Gusau, wacce ya fitar a ranar Juma’a

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Maiduguri, Borno - Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno, ya amince da nadin Barkindo Saidu a matsayin darakta-janar na Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA).

Gwamnan ya kuma nada Malam Abdulkadir Haruna a matsayin babban sakataren Hukumar Ilimin Larabci da Tsangayu ta Jihar Borno (BOSASEB).

Zulum ya sanar da sabbin nade-nade guda 2
Babagana Zulum ya sanar da nadin Barkindo a matsayin daraktan hukumar SEMA. Hoto: @YerwaExpress
Asali: Twitter

Mukamin da Barkindo ya rike a baya kafin nadin da Zulum ya yi masa a yanzu

Kara karanta wannan

‘Yan Siyasa Sun Raba Hankalin Tinubu, Za a Rasa Wanda Zai Zama Minista Daga Bauchi

Nade-naden da Zulum ya yi suna kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa Gwamna Zulum shawara kan harkokin yada labarai, Malam Isa Gusau, ya fitar a ranar Juma’a a a shafinsa na Tuwita.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Barkindo dan kimanin shekaru 54, ya fito ne daga karamar hukumar Gwoza, a yayin da Haruna mai shekaru 59 ya fito daga Ngala.

Barkindo Saidu ya kasance babban sakataren wata hukuma da ke yaki da cutar kanjamau da maleriya a Jihar Borno wato BOSACAM kafin samun wannan mukamin.

Zulum ya ce cancanta ya duba wajen ba da mukamin

Zulum ya ce nadin da aka yi wa Barkindo Saidu ya samo asali ne daga yanayin gogewarsa da kuma kyawawan dabi’un da ya nuna a ayyukansa na baya.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Barkindo ya yi karatuttuka da dama a ciki da wajen Najeriya, inda a shekarar 2019 ya yi digiri na uku a bangaren tsare-tsare a wata jami’a da ke birnin Berlin na kasar Germany.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Nada Tsohon Ministan Shugaba Goodluck Jonathan a Matsayin Sabon SSG

Daga karshe, gwamnan ya taya mutanen biyu murna tare da fatan cewa za su ci gaba da kasancewa masu hidima ga daukacin al’ummar jihar Borno.

Zulum ya nada Tijjani Bukar matsayin sakataren gwamnatin jihar Borno

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan nadin da gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi wa Tijjani Bukar a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar.

Bukar dai tsohon minista a lokacin gwamnatin Jonathan gabanin wucewarsa zuwa majalisar dinkin duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng