Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisar Dattawa Don Ciyo Bashin Dala Miliyan 800 Daga Bankin Duniya

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisar Dattawa Don Ciyo Bashin Dala Miliyan 800 Daga Bankin Duniya

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da wasikar neman izinin ciyo bashi zuwa ga Majalisar Dattawan Najeriya
  • Tinubu a cikin wasikar, ya bukaci majalisar ta sahale masa karbo bashin dala miliyan 800 daga bankin duniya
  • Tinubu ya ce za a yi amfani ne da kudaden da za a ciyo bashin wajen taimakawa ‘yan Najeriya masu rauni da masu karancin abun hannu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

AbujaShugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya aika da takardar neman izinin ciyo bashin dala miliyan 800 daga bankin duniya, zuwa Majalisar Dattawan Najeriya.

Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar shugaban kasar a zaman majalisar na ranar Alhamis kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tinubu zai ciyo bashin dala miliyan 800
Tinubu na neman Majalisar Dattawa ta ba shi izinin ciyo bashin dala miliyan 800 a bankin duniya. Hoto: @officialABAT
Asali: Facebook

Tun a lokacin gwamnatin Buhari ake son ciyo bashin

A cikin wasikar, Shugaba Tinubu ya ce za a yi amfani da bashin da za a ciyo wajen sake inganta shirin ba da tallafi ga mabukata na kasa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Manyan Hafsoshin Tsaron Da Shugaba Tinubu Ya Nada

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a gab da karshen mulkinsa, ya mika wannan bukata ga Majalisar Dattawa ta tara a cikin watan Mayu.

Sai dai majalisar ta 9 ba ta sami damar duba bukatar ba har zuwa lokacin da wa'adinta ya kare a ranar 11 ga watan Yuni.

Tinubu a cikin takardar, ya bayyana cewa daga bankin duniya za a ciyo bashin wadannan kudade kamar yadda aka tsara tun lokacin Buhari.

Abubuwan da za a yi da dala miliyan 800 da Tinubu zai karbo a bankin duniya

Shugaba Tinubu ya ce manufar karbo wannan bashi it ace don tallafawa talakawa da 'yan Najeriya masu rauni da wani dan hasafi da zai taimaka musu wajen warware buƙatunsu na yau da kullun.

Ya bayyana cewa a karkashin shirin na Gwamnatin Tarayyar Najeriya, za a rika ba da naira 8,000 a kowane wata ga talakawa da masu karamin karfi miliyan 12 na tsawon watanni shida.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Nemi Majalisa Ta Sahale Masa Ciyo Bashin Naira Biliyan 500, Ya Bayyana Dalili

Tinubu ya kara da cewa za a rika tura kudaden kai tsaye ne zuwa asusun ajiya na banki da kuma lalitocin wayoyin hannu na wadanda za su ci gajiyar shirin kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Ya kuma ce ana sa ran wannan shiri zai taimaka wajen inganta cimaka, lafiya, ilimi da sauran harkokin rayuwar wadanda za su amfana.

Daga karshe, Tinubu ya ce yana fatan cewa Majalisar Dattawan za ta duba ta kuma amsa wannan bukata ta shi.

Tinubu ya nemi Majalisar Wakilai ta ba shi izinin karbo rancen naira biliyan 500

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan izinin da Shugaba Tinubu ya nema, kan Majalisar Wakilai ta sahale masa ciyo bashin naira biliyan 500.

A cewar Tinubu, za a ciyo bashin ne domin samun kudaden da za a sayawa ‘yan Najeriya kayayyakin tallafi saboda rage musu radadin cire tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng