An Wartaki Dan Majalisa Daga Zauren Majalisar Wakilai Kan Sanya Tufafin Da Basu Dace Ba
- An samu wata 'yar dirama a zauren Majalisar Wakilan Najeriya a zaman da ta gudanar ranar Laraba
- Wani mamba da ba a iya tantance sunansa ba ne ya shiga zauren da wata shiga da ta saɓa ƙa'idar sanya tufafi na majalisar
- Wani mamba daga jihar Edo mai suna Billy Osaweru ne ya ankarar da kakakin majalisar kan irin shigar da ɗan majalisar ya yi
Abuja - An samu wata 'yar ƙaramar dirama a yayinda aka wartaki wani sabon ɗan Majalisar Wakilai daga zauran majalisar, a zamanta na ranar Laraba saboda yin shigar da ba ta dace ba.
Dan majalisar wanda ba a iya tantance ko waye ba, ya shiga zauren majalisar ne sanye da jar riga ƙarama da wando mai ruwan ƙasa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Dan majalisar ya yi wucewarsa abinsa zuwa ɓangaren taron majalisar na wucin gadi, a daidai lokacin da majalisar ke dab da kammala zamanta na ranar Laraba.
Kayan da ya sanya sun saɓawa ƙa'idar sa kaya na majalisar
Jim kadan bayan zaman nasa ne, wani ɗan majalisa mai suna Billy Osaweru, ya ja hankalin kakakin majalisar, kan yadda mamban ya sanya kayan da ba su dace ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce kayan da mamban ya sanya, sun saɓawa ƙa’idar sanya tufafin na majalisar.
Bayan bayyanawa kakakin shigar da ɗan majalisar da ake magana a kansa ya yi, sai aka ga ya miƙe sannan kuma ya fice daga zauren Majalisar Wakilan.
An karanta buƙatar Tinubu ta ciyo bashin naira biliyan 500 a zauren Majalisar Wakilai
Legit.ng ta kawo muku rahoto a zaman da Majalisar Wakilan ta yi a ranar Laraba, kan buƙatar Shugaba Tinubu ta ciyo bashin naira biliyan 500.
Kakakin Majalisar, Abbas Tajuddeen ne ya karanta wasiƙar da shugaban ya aikowa zauren majalisar kan neman sahhalewarsu.
Tinubu a cikin wasiƙar ya bayyana cewa yana so ya yi amfani da kuɗaɗen ne wajen samar da kayayyakin tallafi ga 'yan Najeriya saboda rage raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya jefa su a ciki.
An amince da harshen Hausa a Majalisar Dokokin jihar Bauchi
Legit.ng ta kuma ruwaito muku cewa, Majalisar Dokokin jihar Bauchi, ta amince da amfani da harshen Hausa bayan Turanci, wajen tafiyar da lamurranta.
Kakakin majalisar, Honorabul Abubakar Y Suleiman ne ya sanar da hakan a zaman majalisar na ranar Talata.
Asali: Legit.ng