Shugaba Tinubu Ya Gana da Rukunin Gwamnonin 1999 a Fadar Shugaban Kasa
- Shugaba Bola Tinubu na ganawa yanzu haka da tawagar gwamnonin 1999 a fadar shugaban Najeriya da ke babban birnin tarayya Abuja yau Laraba
- Tinubu na cikin mambobin tawagar waɗanda suka hau mulki a karon farko bayan dawowar mulkin demokuraɗiyya a jamhuriya ta 4
- Tsohon gwamnonin jihohin Delta, Jigawa, Taraba, Filato, Ekiti da Ebonyi da sauran makamantansu sun halarci zaman a Villa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na gana wa yanzu haka da tawagar gwamnonin jihon Najeriya na shekarar 1999 a fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa shugaba Tinubu na ɗaya daga cikin mambobin tawagar gwamnonin waɗanda suka hau kan madafun iko karon farko a 1999.
Gwamnonin su ne rukuni na farko da suka fara zama zaɓaɓɓun gwamnonin jihohi bayan dawowar mulkin demokuraɗiyya a 1999, wanda ake kira da jamhuriya ta huɗu.
Jerin waɗanda suka halarci taron a fadar shugaban ƙasa
Tsoffin gwamnonin da suka halarci wannan zama a Villa yau Laraba sun haɗa da James Ebori na jihar Delta; Donald Duke na jihar Kuros Riba; Niyi Adebayo na jihar Ekiti; da Lucky Igbinedion na jihar Edo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sauran sun ƙunshi Orji Uzor Kalu na jihar Abiya; Sam Egwu na jihar Ebonyi; Chimaroke Nnamani na jihar Enugu; Ibrahim Turaki na Jigawa; Adamu Muazu na jihar Bauchi, da Obong Victor Attah na Akwa Ibom.
Olusegun Osoba na Ogun; Bisi Akande na Osun; Ahmad Yerima na Zamfara; Jolly Nyame na Taraba; Attahiru Bafarawa na Sakkwato da Joshua Dariye na Filato duk suna cikin tsoffin gwamnoni da suka halarci taron.
Daily Trust ta tattaro cewa wannan gana wa na zuwa ne a daidai lokacin da ake dakon ganin mutanen da shugaban ƙasar zai naɗa a matsayin ministoci.
Har yanzu, Tinubu na da sauran akalla makonni buyi ya tura sunayen ministoci ga majalisar tarayya bayan rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Shugaba Tinubu Ya Gana da Sabon Mukaddashin Shugaban EFCC a Villa
A wani labarin na daban kuma Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da muƙaddashin shugaban hukumar yaƙi da masu almundahana ta ƙasa (EFCC).
Wannan ganawa ta ranar Laraba na zuwa ne makonni hudu bayan Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa daga matsayin shugaban EFCC har sai baba ta gani.
Asali: Legit.ng