Tinubu Na Neman Izinin Majalisar Wakilai Wajen Ciyo Bashin N500bn Don Siyawa ‘Yan Najeriya Kayan Tallafi
- Shugaba Tinubu ya aikawa Majalisar Wakilan Najeriya wasikar neman izinin ciyo bashin naira biliyan 500
- Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas ne ya karanta wasikar a zaman majalisar na ranar Laraba
- Tinubu na neman izinin ciyo bashin ne domin sayo kayan agaji wa 'yan Najeriya don rage radadin cire tallafin man fetur
Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aikawa majalisar wakilai wasika, yana neman a yi garambawul kan kasafin kudi na shekarar 2022 domin bas hi damar ciyo bashin naira biliyan 500 don samar da kayyaki na tallafi ga ‘yan Najeriya.
Kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas ne ya karanta wasikar shugaban a zaman majalisar na ranar Laraba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Tinubu zai sayo kayan agaji don rage radadin cire tallafin man fetur
Tinubu a cikin wasikar ya ce bukatar hakan ta zama dole domin bai wa gwamnati damar samar da kayayyaki na tallafi ga ‘yan Najeriya domin rage musu radadin da cire tallafin man fetur ya jefa su ciki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tinubu ya bayyana cewa biliyan 500 kawai yake son ciyowa bashi daga cikin karin sama da biliyan 800 da aka yi a kasafin kudin shekarar 2022.
Ya bukaci a duba bukatar ta sa cikin gaggauta da kuma neman amincewa da ita domin bai wa gwamnatinsa damar samar da kayayyakin jin kai ga ‘yan Najeriya.
Bayan karanta wannan bukata ta shugaban kasa, kakakin ya ce majalisar za ta fara nazarin bukatar a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli.
Tinubu zai bi irin salon Buhari wajen bayyana ministocinsa
Legit.ng ta kawo muku cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, zai bi irin salon tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wajen sanar da ministocin da zai nada.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan a wani taro na 'ya'yan jam'iyyar a Abuja.
Adamu ya ce Tinubu zai fara da aika sunayen ministocin nasa zuwa Majalisar Wakilai, inda bayan an gama tantance su ne zai bayyana mukamin da ya bai wa kowane daga cikinsu kamar yadda Buhari ya yi a farkon wa'adinsa.
APC ta yi magana kan yiwuwar saka sunan Kwankwaso da Wike cikin ministocin Tinubu
Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan uwar jam'iyyar APC ta kasa da ta yi magana kan bai wa Kwankwaso da Wike mukaman minista duk da suna jam'iyyun adawa.
A hirarsa da Channels TV, sakataren jam'iyyar APC na kasa Iyiola Omisore, ya ce akwai yiwuwar jam'iyyar ta su ta fito da tsarin majalisar ministoci ta hadaka.
Asali: Legit.ng