Ta Bayyana: Shugaba Tinubu Zai Bi Irin Salon Buhari Wajen Bayyana Ministocinsa

Ta Bayyana: Shugaba Tinubu Zai Bi Irin Salon Buhari Wajen Bayyana Ministocinsa

  • Jam’iyyar APC ta sanar da yadda shugaban kasa Bola Tinubu zai bayyana ministocinsa da ‘yan Najeriya ke dakon jira
  • Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa Tinubu zai bi irin salon tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • A cewar Adamu, za a aika da sunayen mutanen da ake so a nada ministocin Majalisar Dattawa kafin a nada su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu na kan tattaunawa dangane sunayen ministocinsa da zai nada.

Shugaban jam’iyyar ta APC, Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da shugabannin jam’iyyar na jihohi a Abuja a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Abdullahi Adamu ya bayyana irin salon da Tinubu zai bi wajen nada ministoci
Abdullahi Adamu ya ce Tinubu zai bi irin salon Buhari wajen nada ministocinsa. Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Tinubu na kan tuntubar masu ruwa da tsaki kan batun ministocin

Kara karanta wannan

Sakataren APC Ya Jero Irin Mutanen da Shugaban Kasa Zai Dauko Su Zama Ministoci

Abdullahi Adamu ya ce a yanzu haka Tinubu na kan tuntubar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar dangane da mutanen da yake so ya bai wa mukaman ministocin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Adamu ya kara da cewa da zarar ya kammala tattara sunayen wadanda zai nada, za a aika da su zuwa majalisa domin an tantance su kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Ya ce za a ji sunansu da zarar Tinubu ya mika su zuwa majalisa, inda daga bisani kuma za a rantsar da su bayan tantancewar.

Tinubu zai bayyana ma’aikatar da aka tura kowane bayan tantancewa

Abdullahi Adamu ya kuma kara da cewa Tinubu zai tura da sunayen ne kawai ba tare da bayyana ma’aikatar da zai ba kowanensu ba.

Ya ce sai bayan majalisa ta tantance su ne zai bayyanawa ‘yan kasa inda ya tura kowane daga cikinsu kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.

Kara karanta wannan

Ministocin Bola Tinubu: An Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Irin Wadanda Ya Kamata Ya Bai Wa Mukamai

Wannan wani tsari ne da tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya zo da shi a shekarar 2015 lokacin da yake shirin nada ministocinsa.

A bisa doka, dole ne shugaban kasa ya bayyana ministocinsa da sauran mambobin majalisarsa a cikin kwanaki 60 na farko a ofis.

Saboda haka, shugaba Tinubu na da har zuwa ranar 28 ga watan Yuli kafin bayyana ministocinsa tare da mika sunayensu ga majalisa domin tantance su.

Tinubu ya janyo raguwar kasuwar masu siyar da motoci bayan sanar da sabuwar doka

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan cewa kasuwar masu shigo da tsofaffin motocin da ake kira da ‘Tokunbo’ ko ‘yan kwatano ta ragu da kaso 70%.

Hakan dai ya biyo bayan wata sabuwar dokar haraji da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya kan tsoffin motocin da ake shigowa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng