Shugaba Bola Tinubu Na Daf Da Bayyana Mukamin Da Zai Nada Shugaban Ma'aikatan Jihar Legas
- An rahoto cewa Shugaba Bola Tinubu yana shirin sanar da sabon wanda zai nada mukami, Hakeem Muri-Okunola, Shugaban Ma'aikatan Jihar Legas
- Za a nada Muri-Okunola ne a matsayin babban kebabben sakatare, mukamin da kawo yanzu ba a fayyace ainihin aikinsa ba
- Idan za a iya tunawa Muri-Okunola ya yi aiki a matsayin mataimaki na musamman ga Tinubu a tsakanin 2003 zuwa 2005 lokacin yana gwamnan jihar Legas
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Aso Rock Villa - An rahoto cewa Shugaba Bola Tinubu yana shirin sanar da sabon wanda ya nada mukami kowanne lokaci daga yanzu.
The Cable, a wani wallafa da ta yi na musamman a Twitter a safiyar ranar Laraba, 12 ga watan Yuli, ta bayyana cewa nan ba da dadewa ba Shugaban Kasar zai sanar da Hakeem Muri-Okunola, shugaban ma'aikatan jihar Legas, a matsayin babban kebabban sakatarensa.
Tinubu zai ba wa tsohon hadiminsa mukami
Muri-Okunola ya yi aiki a matsayin hadimi ga Tinubu tsakanin 2003 zuwa 2005, a lokacin yana gwamnan jihar Legas. An saba yi wa Shugaban Ma'aikatan na Jihar Legas lakabi da HMO.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga bisani Tinubu ya nada HMO a matsayin babban sakataren kwamitin amfani da rabon filaye.
HMO daga baya ya zama sakataren dindindin a shekarar 2011 kuma shekaru 10 bayan fara aikin gwamnati an tura shi Ma'aikatar Kasa Da Sifiyo na ofishin gwamna.
HMO ya cigaba da rike mukamin Shugaban Ma'aiktan Jiha tun bayan da ya karbi aiki daga hannun Folashade Adesoye a watan Disambar 2018.
Takaitaccen bayani dangane da Hakeem Muri-Okunola, sabon wanda Shugaba Bola Tinubu zai nada mukami
Wanda ake fatan za a nada mukamin yana da shekara 51 a duniya kuma shine dan fari ga marigayi Mai Shari'a Muritala.
Kawo yanzu ba a fayyace aikin da HMO zai rika yi ba duba da cewa Shugaba Tinubu ya riga ya nada Shugaban Fadar Ma'aikatansa.
Dokar Najeriya ta ba wa Shugaba Bola Tinubu zuwa ranar 28 ga watan Yuli ya sanar da ministocinsa sannan ya tura sunayensu Majalisar Tarayya domin a tantance su.
A cewar doka, dole kowanne shugaban kasa da gwamna ya fitar da sunayen ministocinsa, kwamishinoni da sauran yan fadarsa cikin kwana 60 na farko bayan kama aiki.
Duba wallafar na Twitter a kasa:
Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Nade Biyu Masu Muhimmanci
Tunda farko kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada Olusegun Dada a matsayin mashawarci na musamman kan dandalin sada zumunta.
Hakazalika, Tinubu ya nada Abdulaziz Abdulaziz a matsayin mataimaki na musamman a bangaren jaridu.
Asali: Legit.ng