Ministocin Tinubu: An Shawarci Shugaban Kasa Ya Nada Wadanda Suka Yi Wa APC Hidima a Mukamai

Ministocin Tinubu: An Shawarci Shugaban Kasa Ya Nada Wadanda Suka Yi Wa APC Hidima a Mukamai

  • An shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya fi mayar da hankali wajen nada ‘yan jam’iyyar APC mukamai a gwamnatinsa
  • Wani dan gani kashe nin jam’iyyar ta APC, Buckie Okangbe ne ya bayyana hakan da yake jawabi a Abuja
  • Ya ce jam’yyar tana fama da matsalar raba mukamai ga wasu da basu hidimta ma ta ba su mance da mabiyanta

Abuja - An shawarci Shugaba Tinubu da ya duba ‘ya’yan jam’iyyar APC da suka wahalta ma ta lokacin zaben da ya gabata wajen rabon mukaman siyasa.

Wani babban masoyin jam’iyyar, kuma dan gani kashenin APC, Bukie Okangbe ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Talata, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

An shawarci Tinubu kan wadanda ya kamata ya bai wa ministoci
An bai wa Tinubu shawara kan mutanen da ya kamata ya nada ministoci a gwamnatinsa. Hoto: NTA Network News
Asali: Facebook

Ya taya Tinubu murnar zama shugaban ECOWAS

Buckie wanda shugaban wata kungiyar masoyan APC na kasa ne, ya kuma taya Bola Tinubu murnar zaman shugaban ECOWAS da ya yi a ranar Lahadin da ta gabata.

Kara karanta wannan

Kujerar Shugaban APC Na Tangal-Tangal Bayan Wata 15, Zai San Makomarsa a NEC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce zamowa shugaban ECOWAS da Tinubu ya yi, ya tabbatar da cewa yana gogewar wajen gudanar da ingantaccen shugabanci, wanda zai iya jagorantar Yammacin Afrika ba iya Najeriya kadai ba.

Sai dai a yayin da yake isar da sakon taya murnar, ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya duba ‘yan jam’iyyar da suka ba ta gudummawa sosai wajen samun nasararta a zaben da ya gabata.

Ya nemi Tinubu da ya sauya akalar yadda APC ke rabon mukamai a baya

Buckie ya bayyana cewa ana fama da rashin adalci wajen raba mukami yadda ya kamata a jam’iyyar ta APC, wanda yake fatan Tinubu canjawa akala.

Ya kara da cewa wannan wani abu ne da ya dauki lokaci mai tsawo yana ci musu tuwo a kwarya.

Daga karshe, ya yi wa Tinubu fatan samun nasara a shugabancinsa wajen kawowa Yammacin Afrika ci gaba da ma nahiyar baki daya.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar Labour Ta Yi Azarɓaɓin Faɗin Abin Da Zai Faru a Ƙarshen Shari'ar Obi Da Tinubu

Mutane da dama ciki har da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne suka taya Tinubu murnar zama shugaban ECOWAS.

A cikin sakon taya murna da The Cable ta ruwaito, Buhari ya yi addu’ar samun daidaito da ci gaban tattalin arziki a shugabancin na Tinubu.

Tinubu ya yi wasu manyan sabbin nade-nade guda 2

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan sabbin nade-nade guda biyu da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi bayan dawowarsa taron ECOWAS.

Tinubu ya nada Olusegun Dada mashawarci na musamman kan kafafen sada zumunta, yayin da ya nada Abdulaziz Abdulaziz mataimaki na musamman a bangaren jaridu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng