Shehu Sani Ya Shawarci Tinubu Da Kar Ya Aikata Kurakurai Guda 2 a Gwamnatinsa
- Sanata Shehu Sani ya shawarci Tinubu ya kiyayi aikata manyan kurakurai biyu a gwamnatinsa
- Shehu Sani ya ba Tinubu shawarar ya kiyayi bai wa ministocin Buhari kariya, da kuma bai wa tsoffin gwamnoni mukamai
- Shawarar ta Shehu Sani na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke jiran fitowar ministocin Tinubu
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya kiyayi aikata manyan kurakurai guda biyu a gwamnatinsa.
Shehu ya bayyana hakan ne a shafinsa na sabuwar kafar sada zumuntar nan ta Threads ranar Asabar.
'Yan Najeriya na jiran Tinubu ya saki sunayen ministocinsa
Shawarar ta Shehu Sani na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke ci gaba da zaman jiran fitowar sunayen mutanen da Shugaba Tinubu zai naɗa a matsayin waɗanda da za su yi aiki tare da shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mutane sun yi ta hasashen waɗanda suke tunanin Shugaba Tinubu zai naɗa a matsayin ministoci a gwamnatinsa.
A cikin 'yan kwanakin nan ne aka ji Dele Alake ya fito yana nesanta fadar shugaban ƙasa da wasu sunaye da aka riƙa yaɗa cewa na ministocin ne.
Dele Alake, wanda shi ne mai magana da yawun Shugaba Tinubu, ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Alhamis kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Abubuwa 2 da Shehu Sani ya faɗawa Tinubu ya kaucemawa a gwamnatinsa
1. Shehu Sani ya ce yana da kyau Tinubu ya guji ba da kariya ga tsofaffin ministocin da suka yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin Buhari yayin da aka zo gudanar da bincike a kansu.
2. Sannan Shehu Sani ya kuma bai wa Tinubu shawara kan cewa ya kar ya bai wa tsofaffin gwamnonin da aka tabbatar da sun kwashe dukiyar jihohinsu muƙami a gwamnatinsa.
An nemi Tinubu ya hana Ganduje muƙami ya bai wa Rarara
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan wani ɗan jam'iyyar APC a Kano da ya nemi Shugaba Bola Tinubu ya hana Ganduje muƙami, ya bai wa Rarara a maimakon haka.
Ya ce gudummawar da Rarara ya bai wa APC, ta fi wacce Ganduje ya bai wa jam'iyyar a lokacin zaɓe.
Asali: Legit.ng