Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Karar da Aka Nemi Ta Tsige Gwamnan Delta

Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Karar da Aka Nemi Ta Tsige Gwamnan Delta

  • Kotun ƙoli a Najeriya ta raba gardama kan ƙarar da ake tuhumar gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori
  • Ƙarar wacce aka ɗaukaka har zuwa Kotun ƙoli ta buƙaci a tsige bisa zargin takardun karatun ƙarya ya miƙa wa hukumar zaɓe (INEC)
  • A ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuli, Kotun koli ta kawo karshen gardama, inda ta ƙara tabbatar da hukuncin babbar kotu da kotun ɗaukaka ƙara

FCT Abuja - Kotun kolin Najeriya ta kori ƙarar da aka shigar gabanta wacce ta nemi a soke takarar sabon gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori.

Kwamitin alkai 5 karkashin jagorancin mai shari'a Adamu Jauro ne ya sanar da hukuncin Kotun ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuli, 2023, The Nation ta ruwaito.

Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori.
Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Karar da Aka Nemi Ta Tsige Gwamnan Delta Hoto: Governor Sheriff Oborevwori's media
Asali: Facebook

Wane dalili ya sa aka kai gwamnan ƙara Kotu?

Wanda ya shigar da ƙara, Ikie Aghwarianovwe, ya zargi gwamnan da amfani da takardun karatu na bogi da kuma karya a takardar shekarunsa da ya miƙa wa INEC.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Amarya Yar Shekara 21, Maimunatu Ta Caka Wa Angonta Wuka Har Lahira Kan Karamin Abu a Bauchi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma Kotun koli ta bayyana cewa lauyoyin mai shigar da ƙara sun gaza gansar da Kotu cewa hukuncin Kotunan baya suna yanke kurkure ne.

Kotun Allah ya isa ta kawo karshen shari'ar

Da take yanke hukunci, Kotun daga ke sai Allah ya isa ta tabbatar da hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Asaba da babbar Kotun tarayya.

A rahoton da This Day ta tattara, Mai shari'a Jauro ya ce:

"Bayan nazari mai zurfi kan korafin kowane ɓangare game da batutuwan da ake muhawara a kansu, na fahimci cewa duk inda aka ɗaukaka wannan ƙarar ba zata kai labari ba."
"Babu madogara ko ɗaya. Tun daga tushen ƙarar, da farko ba bu hurumin tsoma baki a lamarin, yanzu kuma kwata-kwata ɓata lokaci ne shigar da ƙarar nan, nima na kori ƙarar."

Kara karanta wannan

Da Sauran Rina: Abba Kyari Zai Cigaba Da Zama Gidan Yari Duk Da Samun Beli, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Ya Yi Sabon Muhimmin Naɗi a Gwamnatinsa, Bayanai Sun Fito

A wani rahoton na daban kuma Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗa Taiwo Oyedele a matsayin shugaban kwamitin tsare-tsare da garabawul ga harkokin haraji.

Kakakin shugaban ƙasa, Dele Alake, ya yi karin bayani kan wanda shugaban ƙasan ya naɗa a matsayin shugaban kwamitin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262