Daga Karshe, Gwamna Adeleke Ya Nada Kwamishinoni a Jihar Osun
- Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya naɗa kwamishinoni a gwamnatinsa kusan watanni 9 bayan hawan kan madafun iko
- Kakakin majalisar dokokin jihar, Kolapo Alimi, ne ya karanta sunayen da ke ƙunshe a wasikar da gwamna ya aiko ranar Jumu'a
- Daga cikin mutane 25 da gwamnan ya naɗa harda tsoffin kwamishinonin tsohon gwamna Rauf Aregbesola, mamban APC
Osun state - Bayan dogon lokaci, gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya naɗa sabbin kwamishinoni karon farko tun bayan hawa karagar mulki a shekarar 2022.
Gwamna Adeleke, wanda ya karɓi rantsuwar kama aiki ranar 27 ga watan Nuwamba, 2022, ya ɗauki tsawon lokaci yana tafiyar harkokin gwamnati ba tare da kwamishinoni da hadimai ba.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa rashin naɗa waɗanda zasu kama masa ya janyo masa suka daga jam'iyyar adawa watau APC.
Gwamna Adaleke ya naɗa tsoffin kwamishinonin Aregbesola
Kamar yadda aka yi tsammani, an ga sunan tsoffin kwamishinoni 2 da suka yi aiki a zamanin mulkin tsohon gwamna, Rauf Aregbesola, babban jigon APC kuma tsohon ministan Muhammadu Buhari.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mutum biyun sune, Mista Kolapo Alimi, da kuma Mista Biyi Odunlade, dukkan su sun riƙe muƙamin kwamishina a lokacin mulkin Aregbesola a jihar Osun.
Cikakken sunayen waɗan gwamnan ya naɗa
A halin yanzu gwamna Adeleke ya tura sunayen sabbin kwamishinoni da mashawarta na musamman ga majalisa watanni 9 bayan hawa kan madafun iko.
Kakakin majalisar dokokin jihar Osun, Adewale Egbedun, shi ne ya karanta sunayen baki ɗaya a zaman majalisa ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuli, 2023.
Rahoton Vanguard ya kawo baki ɗaya sunayen da gwamnan ya tura majalisa, ga su kamar haka:
1. Barista Oladosu Babatunde
2. Prince Bayo Ogungbangbe
3. Mista Sesan Epharaim Oyedele
4. Barista Kolapo Alimi
5. Mista Soji Ajeigbe
6. Mista Moshood Olalekan Olagunju
7. Honorabul George Alabi
8. Honorabul Sunday Olufemi Oroniyi
9. Mista Abiodun Bankole Ojo
10. Dakta Basiru Tokunbo Salami
11. Mista Morufu Ayofe
12. Mista Sola Ogungbile
13. Rabarqn Bunmi Jenyo
14. Misis Ayo Awolowo
15. Barista Wole Jimi Bada
16. Honorabul Dipo Eluwole
17. Alhaji Rasheed Aderibigbe
18. Farfesa Morufu Ademola Adeleke
19. Mistq Adeyemo Festus Ademola
20. Mista Olabiyi Anthony Odunlade
21. Barista Jola Akintola
22. Honorabul Mayowa Adejorin
23. Misis Adenike Folashade Adeleke
24. Mista Tola Faseru
25. Alhaji Ganiyu Ayobami Olaoluwa.
Rigingimun PDP: Dalilin Da Ya Sa Bai Kamata Wike, Makinde Su Koma APC ba
Kuna da labarin Jigon PDP, Bode George, ya roƙi fusatattun gwamnonin G-5 su haƙura su maida wuƙarsu kube kar su sauya sheka zuwa APC gabanin 2027.
Bode George ya ce ita kanta jam'iyyar APC mai mulki tana fama da rigingimun cikin gida amma ba zaune kalau take ba.
Asali: Legit.ng