Rigingimun PDP: Dalilin Da Ya Sa Bai Kamata Wike, Makinde Su Koma APC ba

Rigingimun PDP: Dalilin Da Ya Sa Bai Kamata Wike, Makinde Su Koma APC ba

  • Jigon PDP, Bode George, ya roƙi fusatattun gwamnonin G-5 su haƙura su maida wuƙarsu kube kar su sauya sheka zuwa APC gabanin 2027
  • Jagoran babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa ya bayyana kwarin guiwar cewa PDP zata magance duk wani ƙalubale da ya hanata motsi kuma ta yunkuro
  • A cewar Mista Borde George, ita kanta APC tana fama da rikicin cikin gida domin ba'a raba jam'iyyar siyasa da kace-nace

Tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Chief Bode George, ya gargaɗi mambobin G-5 da suka fusata kar su yi kuskuren sauya sheƙa daga PDP.

Babban jigon ya gargaɗi tsohon gwamnan jihar Ribas kuma jagoran G-5, Nyesom Wike, gwamna Seyi Makinde na Oyo da sauran mambobin tawagar 4 cewa su sauya tunani.

Jigon PDP, Bode George
Rigingimun PDP: Dalilin Da Ya Sa Bai Kamata Wike, Makinde Su Koma APC ba Hoto: Chief Bode George
Asali: UGC

Vanguard ta ce ya yi wannan furucin ne a daidai lokacin da jita-jita ke ƙarfi cewa baki ɗaya mambobin tawagar gwamnonin G-5 na shirin shiga APC gabanin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Babban Jigon PDP Ya Gana da Shugaba Tinubu a Villa, Ya Yi Magana Kan Sauya Sheƙa Zuwa APC

PDP zata murƙushe kalubalen da suka hana ta sakat - George

A wata hira da kafar watsa labaran Arise TV, Bode George ya ce ita kanta jam'iyyar APC mai mulki tana fama da rigingimun cikin gida amma ba zaune kalau take ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kafa hujja da kalaman baya-bayan nan da aka ji shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, na cewa APC ba ruwanta da jagororin majalisa da saka sanar.

Ya ce wannan kalamai da Adamu ya faɗa ƙaɗai ya isa ya gamsar da kowane mutum cewa ba bu wata jam'iyyar siyasa da ke zama kalau babu ɗan rigingimu.

Bisa haka Mista George ya buƙaci mambobi su zauna a haɗu a lalubo hanyar warware matsalolin PDP maimakon su tattara su koma APC.

Tun da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ɗare kan madafun iko a watan Mayu, rahotanni sun nuna cewa Wike ya ziyarci fadar shugaban kasa aƙalla sau 2.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Jam'iyyar APC Ta Tsoma Baki Kan Bidiyon Dala, Ta Aike da Sako Ga Ganduje

Babban Jigon PDP Ya Gana da Shugaba Tinubu a Villa, Ya Yi Magana Kan Sauya Sheƙa Zuwa APC

A wani labarin na daban kuma Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli.

Jim kaɗan bayan ganawar, Fayose ya ce ba zai yi wata-wata ba zai fara caccakar shugaba Tinubu da zaran ya karya alkawurran da ya ɗauka lokacin kamfe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262