Gwamna Lawal Ya Rage Ma'aikatun Jihar Zamfara Daga 28 Zuwa 16
- Gwamnan Zamfara ya tattaba hannu kan wata dokar garambawul wacce ta rage adadin yawan kwamishinonin da zai naɗa
- Dauda Lawal na PDP ya ce dokar zata rage ma'aikatun jihar Zamfara daga 28 zasu dawo 16, kuma ya yi haka ne domin inganta aiki
- A cewarsa, matakin zai taka rawa wajen rage yawan kashe-kashen kuɗin gwamnati kuma mutane zasu ga aiki a ƙasa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya rattaɓa hannu kan dokar zartarwa wacce ta rage yawan ma'aikatun jihar daga 28 sun koma 16 kaɗai.
Gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin sauya akalar ɓangaren aiki ya koma kan turbar amfani wanda al'umma zasu san ana shugabantarsu, a cewar rahoton Leadership.
Dauda Lawal ya ƙara da cewa garambawul din da aka ga yana yi a gwamnatin Zamfara na cikin kudirinsa na rage kashe-kashen kuɗi na ba gaira ba dalili.
Ya ce wannan matakin na daga cikin aniyarsa ta zakulo muƙarrabai na gari waɗan da zasu shayar da mutanen jihar Zamfara romon demokuraɗiyya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A kalamansa, gwamna Dauda Lawal ya ce:
"A wani ɓangaren yunkurin gwamnatina na canja sashin ayyuka ya zama mai amfani kuma ya riƙa aikin da aka buƙata, na sa hannu kan dokar rage yawan adadin ma'aikatu daga 28 yanzu sun koma 16."
"Na yi wannan ne ba don komai ba sai don cika burina na zakulo haziƙan mukarrabai, waɗanda zasu rage yawan kashe-kashen kuɗi kuma su zuba wa al'umma romon demokuraɗiyya."
Abinda ke faruwa a siyasar jihar Zamfara
Dauda Lawal na jam'iyyar PDP ya hau karagar mulkin Zamfara ne bayan lallasa Bello Matawalle na APC, wande ya nemi tazarce a zaben 18 ga watan Maris, 2023.
Tun bayan karban mulki a watan Mayu, gwamna Lawal ya fara ƙorafi da zargin Matawalle da wawure kadarorin gwamnati da suka kai darajar kuɗi masu yawa.
Lamarin dai ya kai ga yan sanda suka je har gidan Bello Matawalle suka kwaso motoci 40, waɗanda gwamnatin Zamfara ke zargin tsohon gwamnan ya sace, Channels tv ta ruwaito.
Majalisa Ta Tabbatar da Nadin Mace Ta Farko a Matsayin Alkalin Alkalan Kano
A wani labarin na daban kuma Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da naɗin mai shari'a Dije Aboki a matsayin shugabar alkalan jihar Kano.
Bayan haka majalisar ta kuma amince da naɗin karin kwamishinoni uku, Ibrahim Fagge, Ibrahim Namadi da Amina Abdullahi-Sani .
Asali: Legit.ng