Majalisa Ta Tabbatar da Nadin Mace Ta Farko a Matsayin Alkalin Alkalan Kano
- Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da naɗin mai shari'a Dije Aboki a matsayin shugabar alkalan jihar Kano
- Wannan ya biyo bayan wasiƙar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike majalisar da kakaki, Ismail Falgore, ya karanta a zaman yau Alhamis
- Bayan haka majalisar ta kuma amince da naɗin karin kwamishinoni uku, Ibrahim Fagge, Ibrahim Namadi da Amina Abdullahi-Sani.
Kano - A karon farko a tarihi, mace ta zama shugabar alkalan jihar Kano bayan naɗin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya mata.
Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da naɗin mai shari'a Dije Aboki a matsayin shugabar alƙalan jiha, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Naɗin mace ta farko a matsayin Alkalin Alkalan Kano ya biyo bayan muhawara kan wasiƙar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya aiko majalisar.
Kakakin majalisar dokokin, Ismail Falgore, ne ya karanta wasikar mai girma gwamna ta neman naɗa mai shari'a Dije a zaman ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun a watan Maris, tsohon gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da mai shari'a Dije Aboki a matsayin shugabar alkalan Kano ta rikon kwarya.
Majalisa ta ƙara tabbatar da naɗin kwamishinoni 3
Bugu da ƙari, majalisar ta amince da naɗin kwamishinoni uku da Abba Kabir Yusuf watau Abba Gida-Gida ya turo domin tantance wa.
Hakan ya biyo bayan tantance mutanen guda uku cikin sauki ba tare da samun tangarɗa ba wanda majalisar ta gudanar duk a zaman yau Alhamis.
Sabbin kwamishinonin da majalisar ta amince da naɗinsu a yau sun ƙunshi, Ibrahim Fagge, Ibrahim Namadi da kuma Amina Abdullahi-Sani.
Da yake jawabi bayan kammala tantance su, Honorabul Falgore ya buƙaci kwamishinonin su tabbatar da cancantarsu ta hanyar sadaukarwa wajen sauke haƙƙin da aka ɗora musu.
Ya kuma roƙe su da su ɗauki darasi daga mai girma gwamna wajen kokarin kawo ci gaba ga jihar Kano, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Kano: Jam'iyyar APC Ta Bukaci Ganduje Ya Yi Fatali da Gayyatar Hukumar Cin Hanci
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta yi fatali da gayyatar da hukumar yaƙi da cin hanci ta tura wa tsohon gwamna Abdullahi Ganduje.
A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban APC da sakatare, jam'iyyar ta buƙaci Ganduje kar ya amsa gayyatar.
Asali: Legit.ng