Bidiyon Dala Na Ganduje Ya Zubda Kimar Kano a Idon Duniya, Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kano
- Hukumar Karbar Korafe-Korafe Da Yaki Da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), ta ce bidiyoyin dala na Ganduje sun taɓa martabar Kano a idon duniya
- Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimingado ne ya bayyana hakan yayin wani taro ranar Laraba a Kano
- Muhuyi ya sha alwashin gudanar da bincike kan fayafayen bidiyon domin dawo da ƙimar jihar Kano a idon duniya
Kano - Hukumar karɓar korafe-korafe Da Yaki Da Rashawa ta jihar Kano (PCACC), ta ce bidiyon dala na tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya lalata martabar jihar a idon duniya.
Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimingado ne ya bayyana hakan, a wani taron wayar da kai kan yaƙi da cin hanci da rashawa kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Bidiyon dalar na Ganduje ya ɓata sunan Kano a wurare da dama
Ya ce rahotanni da dama na nuni da cewa bidiyon dalar na Ganduje, ya jawowa Kano zagi a wurare da dama har zuwa ƙasashen ƙetare.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Muhuyi ya ce a dalilin hakan ne ya sha alwashin ganin ya binciki bidiyon domin dawo da ƙimar jihar Kano a idon duniya.
Ya ƙara da cewa tun lokacin da aka fitar da bidiyon, mutane sun ƙalubalanci hukumar da ta tabbatar da ta binciki tsohon gwamnan don tabbatar da laifinsa ko akasin haka.
Sai dai ya ce hakan bai yi wu ba saboda rigar kariyar da Ganduje yake da ita a lokacin.
Da yaushe aka fitar da bidiyon Ganduje na karɓar Dala?
A shekarar 2018, jaridar Daily Nigerian ta fitar da wasu fayafayen bidiyo na Ganduje da aka yi zargin yana karɓar cin hanci daga hannun ‘yan kwangila.
Ganduje Ya Shiga Tasku a Yayin Da Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta Sake Fara Bincike Kan Bidiyonsa Na Daloli
A cikin faifan bidiyon, an hangi Ganduje na tattara kan dalolin, sannan kuma ya zurara su cikin aljihun babbar rigarsa.
Sai dai Ganduje ya musanta zargin, yana mai cewa fayafayen bidiyon duk na bogi ne.
Binciken ƙwaƙwaf ya bayyana gaskiya kan bindiyon dala na Ganduje
Legit.ng ta kawo muku wani rahoto da Hukumar karɓar korafe-korafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta fitar dangane da bidiyon dala na Ganduje.
Hukumar ta ce binciken ƙwaƙwaf da aka gudanar a kan bidiyon, ya bayyana cewa bidiyoyin ba na bogi ba ne.
Asali: Legit.ng