Peter Obi Yana Cikin Babbar Matsala Yayin Da Tinubu Da Shettima Suka Gabatar Da Shaida Babba a Kotu

Peter Obi Yana Cikin Babbar Matsala Yayin Da Tinubu Da Shettima Suka Gabatar Da Shaida Babba a Kotu

  • Shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, sun gabatar da wata hujja mai karfi a kan Peter Obi, dan takarar jam’iyyar Labour a zaben shugaban kasa na 2023
  • Tinubu da Shettima, sun gabatar da shaida a gaban kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa cewa, Peter Obi ba dan jam’iyyar Labour ba ne a lokacin ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar
  • Hakan ya faru ne yayin da suke kare kansu daga karar da Peter Obi da jam’iyyar Labour, suka shigar na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Birnin Tarayya, Abuja - Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima sun gabatar da wata kwakkwarar hujja a gaban kotu kan Peter Obi, dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar Labour.

Hujjar da Tinubu da Kashim suka gabatar na nuni da cewa Peter Obi baya da rajista a jam’iyyar ta Labour a lokacin da ya tsaya takara, kamar yadda The Nation ta wallafa.

Kara karanta wannan

Jerin Muhimman Takardun Da Tinubu Ya Gabatar A Kotun Zabe Don Kare Kansa Daga Atiku Da Obi

Tinubu da Shettima sun gabata da wata shaida kan Obi
Tinubu da Shettima sun ce Obi ba dan jam'iyyar Labour ba ne lokacin zabe. Hoto: Peter Obi, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Tinubu da Shettima sun yi martani ga Peter Obi

Tinubu da Shettima sun kuma mika kwafin ‘ya’yan jam’iyyar Labour na jihar Anambra domin kara tabbatar da ikirarin na su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A martanin da suka yi wa Obi da jam’iyyarsa ta Labour, Tinubu da Shettima sun yi zargin cewa shi ba dan jam’iyyar Labour ba ne a lokacin zaben shugaban kasa na 2023, kuma yana bukatar hakan domin tsayawa takara a lokacin.

Takardar dai da su Shettima suka gabatar ta hannun lauyansu, Cif Wole Olanipekun (SAN), ta na dauke da kwanan wata 25 ga Afrilu, 2022, wacce ita ce jam’iyyar ta Labour ta aikawa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Rahoton jaridar The Punch ya bayyana cewa Kashim Shettima ya kuma gabatar da takardarsa ta janyewa daga takarar kujerar sanatan Borno ta Kudu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Wasu Manyan Jiga-Jigan PDP 2 a Aso Villa

Lauyan Obi ya ki amincewa da shaidar da aka gabatar

A farkon zaman sauraron shari’ar, Olanipekun ya gabatar da wata takarda ta kariya ga Tinubu da Shettima gaban kotun sauraron kararrakin zaben.

Sai dai lauyan Peter Obi da jam’iyyar Labour, Livy Uzoukwu (SAN), ya ki amincewa da shigar da takardar, amma kotun ta amince kuma ta yi wa takardun biyu alama da RA17 da RA18.

Peter Obi dai na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, wanda Tinubu da Shettima suka yi nasarar zama shugaban kasa da mataimakinsa a cikinsa.

Peter Obi ya bayar da kyautar kudi don gyaran masallatai

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto na dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Labour da ya bayar da kyautar kudi don a gyara masallatai.

Obi ya bayyana cewa kudin da ya bayar, cikon alkawari ne da ya daukarwa musulmi a jiharsa Anambra yayin gudanar da bikin sallah.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito: Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Takardun Karatu Na Jami'ar Chicago a Gaban Kotu

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng