Kotu Ta Soke Korar da Jam'iyyar PDP Ta Yi Wa Tsohon Gwamna, Nnamani

Kotu Ta Soke Korar da Jam'iyyar PDP Ta Yi Wa Tsohon Gwamna, Nnamani

  • Kotun tarayya mai zama a babban birnin tarayya Abuja ta soke korar da aka yi wa tsohon gwamnan Enugu daga PDP
  • Yayin yanke hukunci ranar Litinin, Alkalin Kotun ya ce NWC ba shi da ikon korar tsohon gwamna ko mataimaki ko kuma ɗan majalisa mai ci
  • PDP ta samu matsala da Sanata Chimaroke Nnamani saboda ya zaɓi tallata Tinubu maimakon Atiku a kakar zaɓen 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja, ranar Litinin ta soke matakin da jam'iyyar PDP ta ɗauka kan tsohon gwamnan jihar Enugu, Sanata Chimaroke Nnamani.

Daily Trust ta rahoto cewa kotun ta soke korar da aka yi wa tsohon gwamnan daga jam'iyyar PDP bisa zargin cin amana da zagon ƙasa.

Tsohon sanatan Enugu ta gabas, Chimaroke Nnamani.
Kotu Ta Soke Korar da Jam'iyyar PDP Ta Yi Wa Tsohon Gwamna, Nnamani Hoto: Chimaroke Nnamani
Asali: UGC

Yayin da yake yanke hukunci ranar Litinin, mai shari'a James Omotosho, ya yanke cewa ba'a yi wa Sanata Nnamadi adalci ba duba da tanadin kundin tsarin mulkin PDP.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP a Arewa Ya Shiga Jerin Ministocin da Tinubu Zai Naɗa? Gaskiya Ta Bayyana

Alkalin ya ce idan aka yi la'akari da tanadin sashi na 57 a kwansutushin din PDP, Majalisar zartarwa (NEC) kaɗai ke da ikon kafa kwamitin ladabtarwa amma ba kwamitin gudanarwa ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai shari'a Omotosho ya kara da bayanin cewa NEC kaɗai ke da karfin ikon ladaftar da duk wani mamban PDP da ya taɓa rike kujerar gwamna, mataimaki da ɗan majalisar tarayya.

The Nation ta ruwaito cewa Nnamadi, Sanata mai wakiltar Enugu ta gabas, ya sha kashi hannun ɗan takarar Labour Party, Kelvin Chukwu a zaben 25 ga watan Fabrairu.

Meyasa PDP ta kori tsohon gwamnan daga cikinta?

Idan baku manta ba a taron kwamitin gudanarwa (NWC) karo na 566, jam'iyyar PDP ta kori tsohon sanatan daga inuwarta ranar 10 ga watan Fabrairu bisa zargin cin amana da zagon ƙasa.

Da farko, jam'iyyar PDP ta dakatar da Nnamani kafin daga bisani kuma ta tabbatar da korarsa.

Kara karanta wannan

Ana Shagalin Babbar Sallah, Gwamna Ya Dakatar da Wasu Ma'aikata da Babban Shugaba Nan Take

PDP ta zargi Nnamadi da jingine ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya koma yana yi wa Bola Ahmed Tinubu na APC kamfe gabanin zaɓen 2023.

"Ku Ji Tsoron Allah" Malamai Sun Aike da Sako Ga Shugabannin Siyasa

A wani labarin na daban kuma Manyan malamai da limamai sun aike da saƙo mai matuƙar muhimmanci ga sabbin shugabannin da suka karɓi mulki.

A cewar Malamin, suna roƙon shugabanni da sauran 'yan siyasa da su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin amanar da talakawansu suka ɗora masu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262