Gwamna Otti Ya Dakatar da Shugaban Ma'aikata da Manyan Sakatarori a Abiya

Gwamna Otti Ya Dakatar da Shugaban Ma'aikata da Manyan Sakatarori a Abiya

  • Gwamnan Abiya, Alex Otti na jam'iyar LP ya dakatar da shugaban ma'aikata da baki ɗaya manyan sakatarori
  • A wata sanarwa ranar Alhamis, gwamnan ya ce wannan matakin zai fara aiki ne nan take kana ya naɗa muƙaddashin shugaban ma'aikata
  • Gwamnan ya umarci duk waɗanda matakin ya shafa su miƙa mulki ga babban daraktan ƙasa da su a ma'aikatun da suke

Abia state - Gwamna Alex Otti na jihar Abiya ya dakatar da kusan baki ɗaya manyan Sakatarori da shugaban ma'aikatan jiha a sashin kula da ma'aikata na jihar Abiya.

Premium Times ta tattaro cewa haka na ƙunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Kazie Uko, ya fitar ranar Alhamis, 29 ga watan Yuni, 2023.

Gwamna Alex Otti na Abiya.
Gwamna Otti Ya Dakatar da Shugaban Ma'aikata da Manyan Sakatarori a Abiya Hoto: Alex C Otti/Facebook
Asali: Facebook

Gwamna Otti ya yi bayanin cewa ya ɗauki wannan matakin ne bayan ya rantsar da kwamitin bincike, wanda ya ɗora wa alhakin kwato kadarorin gwamnati da kuɗaɗe.

Kara karanta wannan

Masu Yaɗa Jita-Jitar Gwamnan APC Ya Mutu Sun Shiga Uku, Gaskiya Ta Yi Halinta

Ya ce kwamitin zai yi aikin dawo da kuɗin gwamnati na al'umma wanda ake zargin muƙarraban tsohuwar gwamnatin Okezie Ikpeazu sun yi sama da faɗi da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna ya naɗa mukaddashin shugaban ma'aikatan Abiya

Haka nan kuma gwamna Otti ya amince da naɗin Joy Maduka a matsayin sabon mukaddashin shugabar ma'aikata (HoS) domin maye gurbin wanda aka dakatar.

Misis Joy Maduaka ta yi aiki a matsayin Darakta a ma'aikatar ilimi ta jihar Abiya gabanin wannan sabon muƙami da gwamna ya naɗa ta.

A rahoton Channels tv, wani sashin sanarwan ya ce:

"Mai girma gwamna, Dakta Alex Otti ya dakatar da shugaban ma'aikata da dukkan manyan sakatarorin bangaren ayyuka na jihar Abiya nan take."
"Duk waɗanda wannan matakin ya shafa ana umartansu da su mika ragama ga babban daraktan ma'aikata, sashi da hukumomin da suke aiki."

Kara karanta wannan

Wane Hukunci Aka Ɗauka Kan Kwamishinan Zaben Adamawa Hudu Ari? INEC Ta Fallasa Gaskiya

Bugu da ƙari, sanarwan ta ce dakatarwan da gwamna ya yi zata fara aike ne nan take.

Gwamna Otti ya lashe zaben gwamnan jihar Abiya karkashin inuwar jam'iyyar LP a zaɓen 18 ga watan Maris, 2023.

Ganduje Ya Koka Kan Matakin Abba Gida Gida Na Dakatar da Albashin Ma'aikata 10,000

A wani rahoton na daban kuma Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya koka kan dakatar da albashin ma'aikata sama da 10,000 da ya ɗauka aiki.

Ganduje ya nuna rashin jin daɗinsa bisa matakin da gwamna mai ci, Abba Kabir Yusuf, ya ɗauka kan ma'aikatan a daidai lokacin da ake shirye-shiryen shagalin Sallah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel