Zamu Kama Duk Mai Yada Jita-Jitar Gwamna Akeredolu Ya Mutu, Jam'iyyar APC
- Jam'iyyar APC ta lashi takobin ɗaukar mataki kan masu yaɗa jita-jitar cewa gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya mutu
- Shugaban APC na jiha ya ce masu yaɗa labarin na ƙarya ba su da aikin yi, kuma duk wanda ya shiga hannu zai gane kurensa
- Mako biyu da suka gabata, gwamnan ya ɗauki hutun tafiya jinya ƙasar waje inda ya miƙa harkokin mulki ga mataimakinsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ondo state - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ondo ta ce tana neman kama dukkan masu yaɗa jita-jitar cewa Gwamna Rotimi Akeredolu ya mutu.
Shugaban APC na jihar Ondo, Ade Adetimehin, ya bayyana cewa jam'iyya mai mulki ta shiga damuwa matuƙa kan labaran ƙaryan da ake yaɗawa cewa gwamnan ya kwanta dama.
Mako biyu da suka gabata, gwamnan wanda ke fama da rashin lafiya ya tafi ƙasar wajen hutun jinya na kwanaki 21, bisa haka ya miƙa harkokin mulki ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.
Da yake zantawa da jaridar Punch ranar Alhamis, Mista Adetimehin ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Bamu jin daɗin yadda wasu mutane su ke zama haka nan su wallafa cewa gwamnan mu ya mutu a Intanet, duk labaran da ake yaɗawa ƙarya ce tsantsa, ba mu san meyasa su ke aikata haka ba."
"A matsayin jam'iyya mun shirya fara bin diddigin masu kirkira da yaɗa wannan jita-jita kuma duk wanda ya shiga hannu, babu tantama zamu miƙa shi hannun 'yan sanda."
"Gwamnan mu na nan a raye saboda haka ya kamata masu yaɗa jita-jitar su hakura su dakata tun da wuri."
Mu sanya gwmanan mu a addu'a - Jigon APC
Tun da fari, wani babban jigon APC a jihar Ondo, Chief Olusola Oke, ya yi kira ga mutanen jihar su sanya gwamna Rotimi Akeredolu a cikin addu'o'insu.
Ya ce ya shiga damuwa bisa ganin yadda wasu 'yan siyasa suka ɗauki nauyin yaɗa cewa mai girma gwamna ya riga mu gidan gaskiya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Shugaban INEC Ya Fi Gwamnan CBN Yi Wa 'Yan Najeriya Illa, Bula Galadima
A wani labarin na daban kuma Buba Galadima ya yi kira ga shugaban kasa Tinubu ya kori Farfesa Mahmud Yakubu daga mukamin shugaban INEC.
Ya ce abinda Farfesa Yakubu ya aikata, ya zarce laifukan da dakataccen gwamnan CBN , Godwin Emefiele, ya yi wa 'yan Najeriya muni.
Asali: Legit.ng