Abba Kabir Yusuf Ya Yi Karin Haske Kan Biyayyar Da Yake Wa Kwankwaso
- Gwamna Abba Gida-Gida na jihar Kano ya kare kansa game da biyayyar da yake wa tsohon gwamna Sanata Rabiu Kwankwaso
- Ya ce Kwankwaso na da kwarewa da gogewar da ta cancanci a masa biyayya duba da manyan muƙaman da ya riƙe a ƙasar nan
- Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta dakatar da biyan ma'aikatan da Ganduje ya ɗauka albashi don gudanar da bincike
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano State - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kare kansa kan biyayyar da ake ganin yana yi wa tsohon gwamna, Rabiu Kwankwaso, wanda ake tunanin tamkar ya zama ɗan amshin shata.
Yusuf, wanda ya fi shahara a bakunan mutane da Abba Gida-Gida, ya yi ƙarin haske kan wannan batu ne yayin rantsar da sabbin kwamishinoni a gidan gwamnati ranar Litinin.
Shin dagaske ya zama ɗan amshin shatan Kwankwaso?
Abba Gida-Gida ya ce gogewar Kwankwaso a matsayin wanda ya riƙe kujerar gwamna, Sanata da Minista ya cancanci zama jogoran da za'a yi wa biyayya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Channels tv ta rahoto a kalamansa yana cewa:
"Ya riƙe kujerar gwamnan jihar Kano, ministan tarayyan Najeriya kuma tsohon Sanata, ya zama wajibi mu amfana da gogewarsa. Kwankwaso ya cancanci zama jagora na kuma ina alfahari da zama mai masa biyayya da ɗa'a."
Meyasa gwamnatin Kano ta dakatar da albashin ma'aikata 10,700?
Da yake ƙarin haske kan wannan, gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ta cimma matsayar dakatar da albashin waɗan nan ma'aikata da aka ɗauka a mulkin tsohon gwamna Ganduje.
Ya kuma caccaki tsohuwar gwamnatin bisa abinda ya kira kulla makirci da tuggun daɗin nauyi ga gwamnatin mai zuwa ta hanyar ɗaukar sabbin ma'aikata 10,700.
"Sun ɗauki sabbin ma'aikata 10,700 na ba gaira babu dalili domin ƙara wa gwamnatinmu nauyi amma mun san yadda zamu magance matsalar."
"A halin yanzu dai mun dakatar da biyansu albashi har sai bayan mun kammala bincike."
Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi Manyan Naɗe-Naɗe 2 a Karon Farko
A wani labarin kuma Sanata Godswill Akpabio ya yi sabbin manyan naɗe-naɗe guda biyu karon farko tun bayan lashe zaɓen shugaban majalisar dattawa.
Akpabio, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom ya naɗa shugaban ma'aikatansa da kuma mataimaki ranar Litinin 26 ga watan Yuni, 2023.
Asali: Legit.ng