Abbas, Sabon Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya Ya Nada Sabbin Hadimai 33
- Sabon kakakin majalisar wakilan tarayya, Honorabul Tajudeen Abbas, ya yi sabbin naɗe-naɗen hadimai 33
- Abbas ya naɗa masu ɗaukar rahoto na manyan jaridu biyu a matsayin hadimai ranar Litinin 26 ga watan Yuni, 2023
- A sanarwan da mai magana da yawun Abbas ya fitar, ya ce naɗe-naɗen zasu fara aiki ne nan take
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Kakakin majalisar wakilan tarayya, Tajudeen Abbas, ya naɗa mai kawo rahoto a jaridar Punch, Leke Bayeiwu, a matsayin babban sakataren watsa labarai.
Leke na ɗaya daga cikin sabbin hadimai 33 da sabon shugaban majalisar wakilan ya naɗa ranar Litinin, 26 ga watan Yuni, 2023, kamar yadda Daily trust ta tattaro.
Har zuwa yau da Abbas ya naɗa shi muƙami, Leke ya kasance mai ɗauko rahoton Punch a zauren majalisar tarayya da ke birnin tarayya Abuja.
Wasu daga cikin mutanen da Abbas ya naɗa a matsayin hadimansa
Haka zalika, kakakin majalisar wakilan ya naɗa mai ɗaukar rahoto a gidan jaridar Daily Independent, Ahmed Baba Musa, a matsayin mai taimaka masa na musamman kan midiya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Musa yana wa kamfanin jaridarsa aiki a zauren majalisar tarayya gabanin wannan sabon muƙami da ya samu daga Tajudeen Abbas.
Mai magana da yawun kakakin majalisar wakilai ta ƙasa, Musa Abdullahi Krishi, shi ne ya sanar da waɗan nan sabbin naɗe-naɗe a wata sanarwa da ya aike wa manema labarai ranar Litinin.
Yaushe sabbin hadiman zasu fara aiki?
A rahoton da jaridar Leadership ta kawo, sanarwan ta ƙara da bayanin cewa waɗan nan naɗe-naɗen 33 zasu fara aiki ne nan take.
Idan baku manta ba Abbas, wanda ya samu goyon bayan APC da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya samu nasarar zama kakakin majalisar wakilan tarayya ta 10 ranar 13 ga watan Yuni.
Ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Zariya daga jihar Kaduna ya samu kuri'u 253 wanda suka bashi damar lallasa abokan karawarsa da gagarumin rinjaye.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godwin Akpabio, Ya Yi Nadin Farko Bayan Cin Zabe
A wani rahoton na daban kuma Sanata Godswill Akpabio, ya yi naɗin farko tun bayan lashe zaɓen shugaban majalisar dattawa ta 10.
Sanata Akpabio ya amince da naɗin Barista Sylvester Okonkwo, a matsayin shugaban ma'aikatansa. Haka nan kuma ya naɗa mataimakin shugaban ma'aikatan.
Asali: Legit.ng