Wata Sabuwa: Babban Dan Kwankwasiyya Ya Soki Rusau Da Abba Gida Gida Ke Yi A Kano, Ya Ce Ba Daidai Ba Ne
- An umarci gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya dakata da rusau na gine-gine da yake gudanarwa a jihar
- Kotun tarayya ce ta bayar da umarnin dakatarwar biyo bayan karar da wani lauya kuma dan asalin Kano, Saminu Muhammad ya shigar a kan gwamnan
- Da yake mayar da martani, wani dan gani kasha nin Kwankwaso, Alhaji Sunusi Balarabe, ya yi Allah-wadai da matakin da gwamnan ya dauka
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - Babbar kotun tarayya da ke Kano, ta dakatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ci gaba da rusa gidaje da sauran gine-gine da yake yi a jihar.
Mai shari’a S.A. Amobeda ne ya bayar da wannan umarni, biyo bayan karar da wani lauya kuma dan asalin Kano Saminu Muhammad ya gabatar a gabansa, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Kotu ta dakatar da gwamnan Kano daga ci gaba da rusa gine-gine
A wani hukunci da kotun ta yanke a ranar Juma’a, 22 ga watan Yuni, ta dakatar da gwamnan da kuma jami’ansa ci gaba da rusau da suke yi a hanyar BUK, kamar yadda rahoton Channels TV ya nuna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kotun ta ba da umarnin a dakatar da rusau din har zuwa lokacin da za ta gama yanke hukunci.
Dan a mutun Kwankwaso ya soki matakin rusau na Abba Gida
Da yake mayar da martani game da wannan rusau din, babban dan darikar Kwankwasiyya a Kano, Sanusi Balarabe, ya koka kan yadda gwamnatin Abba ke ci gaba da rusa gine-gine ba kakkautawa.
Ya ce wannan mataki na rusau da Abba ya dauka kuskure ne, inda ya shawarce shi da ya dakata, sannan ya tsaya ya yi abinda ya kamta, kamar yadda The Guardian ta ruwaito.
A kalamnsa:
“A gaskiya, babu daya daga cikinmu da ya zabi wannan gwamnati domin ta aiwatar da irin wadannan ayyuka na rushe-rushe.”
Alhaji Sanusi ya kara da cewa duk rushe-rushen da Abba yake yi ‘yan Kano yake janyowa asara ba ‘yan wani waje ba.
Ya shawarci gwamnan da ya rika mayar da kadarorin hannun gwamnati ne, maimakon ya yi ta ruguje su.
Matasa sun fito zanga-zangar adawa da rusau din da Abba Gida Gida yake yi
A wani labaari da Legit.ng ta wallafa a baya, kun karanta cewa a ranar Litinin ne aka tashi da wata zanga-zanga da daruruwan matasa suka gudanar a Kanon Dabo.
Zanga-zangar dai an gudanar da ita ne domin nuna adawa da aikin rusau din da gwamnati mai ci ta Abba Gida Gida ke yi.
Asali: Legit.ng