APC Ta Shirya Kwace Sanatan Kaduna Ta Tsakiya a Hannun PDP, Ta Gabatar Da Manyan Shaidu 6

APC Ta Shirya Kwace Sanatan Kaduna Ta Tsakiya a Hannun PDP, Ta Gabatar Da Manyan Shaidu 6

  • Ɗan takarar sanatan APC, Muhammad Sani Abdullahi, ya gabatar da shaidu shida domin ƙalubalantar nasarar ɗan takarar PDP
  • Kotun ta saurari shaidun da aka samo daga makarantun da ɗan takarar PDP ya halarta da hukumar INEC
  • A zaɓen dai hukumar INEC ta sanar da ɗan takarar jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen sanatan Kaduna ta tsakiya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Ɗan takarar sananta jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Muhammad Sani Abdullahi, ya gabatar da shaidu shida domin ƙalubalantar nasara da takardun ɗan takarar PDP, Lawal Adamu wanda aka fi sani da Mr LA.

Kotun mai alƙalai uku a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a HH Kereng, ta saurari bayanan shaidun waɗanda suka fito daga makarantun da ɗan takarar PDP ya halarta da hukumar shirya zaɓe ta INEC.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Mayar Da Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Arewa Da Aka Tsige Kan Mukaminsa

APC ta gabatar da shaidu domin kalubalantar nasarar dan takarar Sanatan PDP a Kaduna ta tsakiya
Muhammad Sani Abdullahi yana ƙalubalantar nasarar Lawal Adamu Hoto: Muhammad Sani Abdullahi Dattijo, Lawal Adamu Usman
Asali: Facebook

Shaidun APC 6 sun bayar da shaida akan ɗan takarar PDP

Nigerian Tribune ta rahoto cewa jami'ar Ahmadu Bello, Zaria (ABU) ita ce ta fara bayar da shaida inda ta samu wakilcin ɗaya daga lauyoyinta, Abubakar Is’haq daga tsangayar ilmin shari'a na jami'ar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An gayyato jami'ar ne domin ta bayar da takardun bayanan Lawal Adamu lokacin da yake matsayin ɗalibi a jami'ar.

Shaida ta biyu, hukumar shirya jarabawa ta ƙasa (NECO) wacce ta samu wakilcin darektan ayyukan na musamman Esther Bala Wuyaa, ta gabatar da haƙiƙanin takardar da ke tabbatar da sakamako a gaban kotu, cewar rahoton The Punch.

Shaida ta uku shi ne shugaban makarantar Demonstration Primary School, Dr. Ibrahim Yusuf, wanda ya gabatar da rajistar makarantar daga 1982 zuwa 1986 wanda ya nuna babu bayanan Lawal Adamu Usman a matsayin ɗalibin makarantar.

Kara karanta wannan

Yadda Peter Obi Ya Ci Amanar Atiku Abubakar Gabanin Zaben Shugaban Kasa Na 2023, Sabbin Bayanai Sun Fito

Da yake bayar da shaida a gaban kotun, shugaban makarantar sakandiren Government Day Secondary School (GDSS), Gwagwalada, Bello Suleiman, ya ce babu bayanan Lawal Adamu Usman a matsayin ɗalibin makarantar daga 1986 zuwa 1994 kamar yadda yake iƙirari.

An kuma kira ƙarin wasu shaidu biyu ciki har da na hukumar INEC waɗanda suka gabatar da shaidunsu a gaban kotu.

Kotun ta karɓi bayanansu a matsayin shaida

Dukkanin makarantun da suka bayar da shaida sun miƙa takardun rajistarsu ga kotun a matsayin shaida.

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar har sai zuwa ranar, 11 ga watan Yulin 2023 domin ci gaba da karɓar shaidu kan ƙarar satifiket ɗin bogi da ake yi wa wanda ake ƙara.

Alkalin Kotun Zabe Ya Gargadi Melaye

A wani labarin kuma, alƙalin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, Haruna Tsammani ya ja kunnen wakilin tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Dino Melaye.

Kara karanta wannan

An Rage Mugun Iri Bayan Jami'an Tsaro Sun Sheke 'Yan Bindiga Masu Yawa a Arewacin Najeriya

Alƙalin ya tunatar da Melaye kotun ba wurin wasa bane bayan an yi masa tambayoyi ya kama kwane-kwane yana ƙin amsa tambayoyin da aka yi masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng