Gwamna Aliyu Ya Kori Sakatarorin Ilimi Na Kananan Hukumomi 23 a Sakkwato
- Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya kori Sakatarorin ilimi na kananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar
- Wannan na zuwa ne yayin da shugaban makarantar Firamaren Sabon Birni ya bayar da shaida a gaban Kotun ƙarar zaben gwamna
- Rahoto ya nuna shugaban makarantar ya ba
- da shaidar da ke nuna mataimakin gwamna bai yi makarantar ba kamar yadda ya yi ikirari
Sokoto - Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato ya kori Sakatarorin ilimi na kananan hukumomi 23 da ke jihar, kamar yadda rahoton jaridar Vanguard ya kawo.
Gwamnan ya umarci baki ɗaya Sakatarorin da korar ta shafa su miƙa jagorancin hukumomin ilimin ga manyan ma'aikatan Ofis ɗinsu a kananan hukumomin.
Sakataren watsa labaran mai girma gwamnan Sakkwato, Abubakar Bawa, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 21 ga watan Yuni.
Ya ƙara da bayanin cewa wannan matakai na korar shugabannin zai fara aiki ne nan take.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Meyasa gwamnan ya ɗauki wannan mataki?
Rahoton Leadership ya yi ikirarin cewa wannan yunkurin na gwamna na zuwa ne a daidai lokacin da ake sauraron shaidu a kotun sauraron ƙorafe-korafen zaben gwamnan jihar Sakkwato.
Bayanai sun nuna shugaban makarantar Firamare ta Sabon Birni da ke karamar hukumar Sabon Birni, Ibrahim Abdullahi, ya halarci zaman Kotun a matsayin shaida.
Kotun ta gayyace Malam Abdullahi, ya bada shaida a ƙarar da ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, Sa’idu Umar, ya shigar yana kalubalantar nasarar Aliyu a zaɓen 2023.
Umar ya yi ikirarin cewa mataimakin gwamna Aliyu, Mohammed Idris Gobir, bai cancanci tsayawa takara ba bisa hujjar cewa bai yi makarantar Firamare ba.
Lauyan ɗan takarar gwamnan PDP, S.I. Ameh (SAN) ne ya gabatar da Malamin makarantar wanda ya nuna wa Kotu bayanan waɗanda suka kammala Firamare tun daga 1981-1987.
Shugaban makarantar ya gabatar da tarin takardun ne a matsayin shaidar da ke tabbatar da cewa Gobir bai halarci Makarantar Firamaren ba kamar yadda ya yi ikirari.
Haka nan a lokacin tambayoyi, Malam Abdullahi ya faɗa wa Kotu cewa shi ne shugaban makarantar na yanzu kuma ya yi bayanin cewa an sauya sunan Firamaren daga Town Primary School zuwa Model Primary School.
Korar sakatarorin da gwamna Aliyu ya yi a ranar da aka saurari wannan shaida a Kotu ya sa ana ganin wani yunkuri ne na kare aukuwar irin haka nan gaba domin shi kansa yana fama da Kes ɗin rashin yin makaranta.
Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince da Naɗin Kwamishinoni 16 Cikin 19
A wani rahoton kuma Majalisar dokokin jihar Kano ta tantance kwamishinoni 16 cikin 19 da gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura mata.
Bayan kammala tantance mutane 16 cikin 19, majalisar ta amince tare da tabbatar da sabbin kwamishinonin a kudirin da shugaban masu rinjaye, Lawal Hussaini, ya gabatar.
Asali: Legit.ng