Gwamna Makinde Ya Tura Sunayen Kwamishinoni 7 Ga Majalisar Dokokin Oyo

Gwamna Makinde Ya Tura Sunayen Kwamishinoni 7 Ga Majalisar Dokokin Oyo

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, na jam'iyyar PDP ya tura wa majalisar dokokin jihar sunayen kwamishinoni 7 da ya naɗa
  • Rahoto ya nuna cewa sakon gwamnan ya isa majalisar bayan tashi daga zaman ranar Talata amma za'a karanta sunayen ranar Alhamis
  • Mutum shida daga ciki duk sun yi aiki da Makinde a zangon mulkinsa na farko yayin da aka samu sabuwar fuska guda ɗaya

Oyo - Matukar ba'a samu wani sauyi a mintunan karshe ba, majalisar dokokin jihar Oyo zata karɓi jerin sunayen sabbin kwamishinoni 7 da zasu yi aiki a matsayin mambobin majalisar zartarwa.

Rahoton The Nation ya tattaro cewa gwamna Seyi Makinde, ne ya tura sunayen kwamishinoni da ya naɗa ranar Talata kuma ana tsammanin majalisar zata faɗe su ranar Alhamis.

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
Gwamna Makinde Ya Tura Sunayen Kwamishinoni 7 Ga Majalisar Dokokin Oyo Hoto: Seyi Makinde
Asali: Twitter

Kamar yadda ya yi alkawari, daga cikin waɗanda gwamnan ya zakulo domin naɗa su a matsayin kwamishinoni harda tsofaffin da suka yi aiki da shi a zangon mulkin farko.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Haramta Ayyukan 'Yan Acaba a Babban Birnin Jiha, Ya Faɗi Dalilai

Idan zaku iya tunawa, gwamna Makinde na jihar Oyo ya sha alwashin sake dawo da waɗanda suka yi abin a yaba a zangon farko domin su ɗora daga inda suka tsaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya mai kusanci da majalisar dokokin Oyo, ta tabbatar da cewa sunayen sun iso ranar Talata bayan kammala zama shiyasa ba'a karanta sakon ba.

Su waye gwamna Makinde ya sake dawo da su?

Wasu daga cikin tsoffin kwamishinonin da Makinde ya dawo da su sun haɗa da ɗan tsohuwar kakakin majalisar Oyo, Sanata Monsurat Sunmonu da Seun Ashamu, wanda ya yi aiki a ma'aikatar makamashi.

Sauran waɗanda suka dawo su ne, Akinola Ojo, Farfesa Musibau Babatunde, Faosat Sanni, Farfesa Daud Sangodoyin, da kuma Adeniyi Adebisi.

Sabuwar fuskar da aka gani a cikin jerin kwamishinonin ita ce kodinetan mata a tawagar kamfen Omi Titun 2.0, Misis Toyin Balogun.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 35 da Wasu Hadimai da Ya Naɗa

Majiyar ta ƙara da cewa a ranar Alhamis, za'a karanta sunayen kwamishinonin yayin da tantance su kuma zai biyo baya.

Gwamna Nwifuru Na Ebonyi Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 35 da Wasu Hadimai

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Ebonyi ya ba wa sabbin kwamishinoni 35 rantsuwar kama aiki a matsayin mambobin majalisar zartarwa.

Yayin wannan bikin, Gwamnan na jam'iyyar APC ya buƙace su da su kawo sabbin abubuwa da dabarun sauke nauyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262