Gwamna Yusuf Ya Umarci Kwamishinonin da Ya Nada Su Bayyana Dukiyar da Suka Mallaka

Gwamna Yusuf Ya Umarci Kwamishinonin da Ya Nada Su Bayyana Dukiyar da Suka Mallaka

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya umarci kwamishinonin da ya zaɓa su gaggauta bayyana abinda suka tara
  • Abba Gida-Gida ya lashi takobin cewa ba zai rantsar da duk wanda ya yi fatali da Fam ɗin bayyana dukiyar da ka mallaka ba
  • Wannam umarni ya shafi sauran waɗanda suka riga suka dafi madafun iko a gwamnatin Abba, inji sanarwan

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci dukkan kwamishinoni da ya naɗa su hanzarta yin biyayya ga dokoki da ƙa'idojin aiki wanda ya zama tilas.

Gwamna Yusuf ya ce daga yanzu, duk wanda ya san sunansa ya shiga cikin waɗanda za'a naɗa kwamishina ya bayyana dukiyar da ya mallaka gabanin majalisa ta tantance shi.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Gwamna Yusuf Ya Umarci Kwamishinonin da Ya Nada Su Bayyana Dukiyar da Suka Mallaka Hoto: channelstv
Asali: UGC

Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya faɗi haka ne a cikin wata gajeruwar sanarwa da gwamnatin Kano ta fitar ranar Laraba, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Haramta Ayyukan 'Yan Acaba a Babban Birnin Jiha, Ya Faɗi Dalilai

Abba Gida Gida ya sha alwashin cewa duk kwamishinan da ya kauce wa cike Fam din bayyana dukiya daga hukumar kula da ƙa'idojin aiki, ba zai rantsar da shi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Muna kira ga baki ɗaya sauran naɗe-naɗen da muka yi a wannan gwamnati su yi biyayya ga wannan umarni," in ji gwamnan.

Gwamna Yusuf ya jaddada kudirinsa ga al'ummar jihar Kano, inda aka ji yana cewa gaskiya da kiyaye haƙƙin sauke nauye ne zasu zama alkiblar gwamnatinsa.

A cewarsa, ta haka ne kaɗai zai cika alkawarin da ya ɗauka a kakar zaɓe da kuma abinda ke cikin kundin manufofinsa na kafa nagartacciyar gwamnati da kowa zai yi na'am da ita, PM News ta rahoto.

Umarnin gwamnan na zuwa ne awanni kaɗan bayan ya yi barazanar fallasa sunayen dukkan waɗanda suka yi kashe mu raba da kadarorin gwamnati a lokacin mulkin Ganduje.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 35 da Wasu Hadimai da Ya Naɗa

Abba Gida Gida Ya Aike da Sunayen Kwamishinoni 19 Ga Majalisar Dokokin Kano

A rahoton mu na jiya kun ji cewa Abba Gida-Gida ya tura wa majalisar dokokin jihar Kano sunayen kwamishinoni 19 da yake shirin naɗawa su kama aiki.

Kakakin majalisa, Isma'il Falgore, ya karanta sunayan kwamishinonin da mai girma gwamna ya aiko a zaman ranar Talata kuma mun kawo muku su baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262