Ranar Da Shugaba Tinubu Zai Iya Mika Sunayen Ministocinsa a Gaban Majalisa Ta Bayyana
- Gwamnonin da ke kan mulki, tsaffin gwamnoni da jiga-jigan ƴan jam'iyyu na ta ƙoƙarin miƙa sunayen ministoci ga Shugaba Tinubu
- Mambobin jam'iyyar New Nigeria People's Party (NNPP) da Peoples Democratic Party (PDP) na faɗi tashin ganin sun shiga cikin jerin ministocin
- Majiyoyi sun bayyana cewa ana saran Tinubu zai miƙa sunayen ministoci ga majalisar dattawa lokacin da ta dawo zamanta a ranar 4 ga watan Yuli
FCT, Abuja - Wani sabon rahoto ya nuna cewa akwai yiwuwar Shugaba Bola Tinubu ya tura sunayen ministocinsa ga majalisar dattawa bayan ranar 4 ga watan Yulin 2023.
A satin da ya gabata, majalisar dattawa ta ɗage zamanta har zuwa ranar Talata, 4 ga watan Yuli, cewar rahoton The Guardian.
Rigima yayin da shugabannin APC ke kokowar samun gurabe a jerin ministoci
A lokacin da majalisar za ta ci gaba da zamanta, ana saran Shugaba Tinubu ya kammala haɗa sunayen ministocinsa domin miƙa wa a gaban majalisar ta tantancesu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ƴan siyasa na ci gaba da faɗi tashi domin ganin sun samu gurabe a cikin ministocin Shugaba Tinubu. Gwamnoni da ke kan mulki, tsaffin gwamnoni da jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ta kokawar ganin sun samu gurabe a cikin ministocin.
A cewar rahoton Vanguard, kamun ƙafar bai tsaya kawai a ƴan jam'yyar APC ba.
Jiga-jigan jam'iyyun adawa irinsu Peoples Democratic Party (PDP) da New Nigeria People's Party (NNPP) su ma suna da muradin samun gurabe a cikin ministocin.
Amma shugabannin APC basu goyon bayan hakan. Daga cikin ƙorafin da jiga-jigan na APC su ke kawo wa shi ne halastattun ƴan jam'iyyar APC kawai yakamata a zaɓa a matsayin ministocin.
Muhimman Wuraren Da Shugaba Tinubu Ya Kawo Sauyi
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa tun bayan rantsar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kawo sauye-sauye a wurare da dama a ƙasar nan.
Fannin tattalin arziƙi na daga cikin wuraren da sabon shugaban ƙasar ya fara durfafa domin kawo sauyi a cikinsa, saboda rawar da yake takawa wajen ci gaban ƙasa.
Asali: Legit.ng