Mambobi Sun Zabi Sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo da Mataimaki

Mambobi Sun Zabi Sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo da Mataimaki

  • Gwamna Obaseki ya rantsar da majalisar dokokin jihar Edo ranar Jumu'a, 16 ga watan Yuni, 2023 a Benin, babban birnin Edo
  • Bayan rantsarwar da magatakarda ya yi a madadin gwamna, mambobi sun zaɓi Blessing Agbebaku, a matsayin sabon kakaki
  • Haka zalika sun zaɓi yar majalisa mace a matsayin mataimakiyar shugaban majalisar dokokin Edo ta 8

Edo State - Honorabul Blessing Agbebaku, mamba mai wakiltar mazaɓar Owan ta yamma ya samu nasarar zama sabon kakakin majalisar dokokin jihar Edo ranar Jumu'a 16 ga watan Yuli, 2023.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Honorabul Agbebaku ya riƙe muƙamin shugaban ma'aikatan tsohon kakakin majalisar dokoki da ya gabata, Marcus Onobun.

Sabon kakakin majalisar Edo, Blessing Agbebaku.
Mambobi Sun Zabi Sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo da Mataimaki Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Mambobi sun zabi sabon kakakin ne jim kaɗan bayan magatakardan majalisa, Yahaya Omogbai, ya shelanta rantsar da majalisa ta 8 a madadin gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo.

Kara karanta wannan

Sabon Ɗan Majalisa Kuma Matashi Ya Samu Nasarar Zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar APC

Mambobi sun zaɓi mace a matsayin mataimakiyar kakakin majalisa

Haka zalika majalisar ta zaɓi Misis Maria Edekor, mamba mai wakiltar Esan Ta Arewa maso Gabas II a inuwar PDP a matsayin mataimakiyar kakakin majalisa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton Leadership ya nuna cewa an kuma rantsar da mambobi 24 a majalisar dokokin Edo ta 8 ranar Jumu'a.

Zamu haɗa kai domin ci gaban jihar Edo - Sabon kakaki

Da yake jawabi jim kaɗan bayan rantsuwar kama aiki, Agbebaku ya yi alƙawarin haɗa kan mambobin majalisar domin ci da jihar Edo gaba.

Ya kuma ƙara gode wa Allah bisa tsari da kariyar da ya ba shi har aka kammala zaɓe kuma ya samu nasarar zama kakakin majalisar dokoki ta 8.

A kalamansa ya ce:

"Zaɓe na a matsayin wanda zai jagoranci majalisa wani girma ne da alfarma, wanda ya nuna kun aminta da ni. Ba zan yi wasa da wannan matsayi ba, zan tafi da kowa ba tare da nuna banbancin jam'iyya ba."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: APC Ta Rasa 1, Gbaja Ya Yi Murabus Daga Majalisar Wakilan Tarayya

Shugaba Tinubu Ya Kafa Tarihi, Ya Kara Motocin Kashe Gobara a Ayarinsa

A wani rahoton na daban kuma Shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya amince da sanya motocin kashe gobara a cikin ayarin tawagar shugahan ƙasa.

Shugaban hukumar kashe gobara ko hukumar kwana-kwana (FFS) na ƙasa, Injiniya Abdulganiyu Jaji, shi ne ya sanar da haka a birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262