Majalisar Dokokin Kano Ta Amince da Bukatar Abba Gida-Gida Ya Nada Hadimai 20

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince da Bukatar Abba Gida-Gida Ya Nada Hadimai 20

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi kira da Abba Gida-Gida ya aike da wasiƙar neman naɗa hadimai 20 ga majalisar dokokin jihar
  • Kakakin majalisar dokokin jihar, Isma'il Falgore, ya karanta takardar mai girma gwamna a zaman mambobi na yau Laraba, 14 ga watan Yuni, 2023
  • Bayan nazari kan bukatar gwamna Abba Gida-Gida da kaɗa kuri'a tsakanin yan majalisu, majalisar ta sahalewa gwamna ya naɗa mutane 20

Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da bukatar gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya naɗa mashawarta na musamman guda 20.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da mataimakin kakakin majalisar, Muhammad Butu (NNPP-Rimingado/Tofa) ya gabatar yayin zaman majalisar ranar Laraba.

Zauren majalisar dokokin jihar Kano.
Majalisar Dokokin Kano Ta Amince da Bukatar Abba Gida-Gida Ya Nada Hadimai 20 Hoto: dailynigerian
Asali: UGC

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa Zubairu Masu, mamba mai wakiltar Sumaila a inuwar NNPP mai kayan marmari ya fara goyon bayan kudurin nan take.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: APC Ta Rasa 1, Gbaja Ya Yi Murabus Daga Majalisar Wakilan Tarayya

Daga nan dukkan mambobi suka kaɗa kuri'ar amincewa bayan kakakin majalisar dokokin, Isma'il Fargore, ya buɗe fagen kaɗa kuri'a da murya, jaridar Gazette ta tabbatar a rahotonta

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasiƙar da Abba Gida-Gida ya aike wa majalisar dokokin Kano

A jawabinsa, Honorabul Falgore ya karanta wasiƙar da gwamna Abba ya aiko majalisar, inda ya buƙaci ta sahale masa ya naɗa masu ba shi shawara ta musamman guda 20.

Kakakin ya kara da cewa amincewar majalisar zata bai wa Abba Gida-Gida damar naɗa waɗanda zasu taimaka masa wajen aiwatar da kyawawan tsaruka da shirye-shirye ga al'ummar Kano.

"Mai girma gwamna ya nemi amincewar majalisa ya naɗa masu ba da shawara ta musamman waɗanda zasu taimaka masa ya aiwatar da kudirori da tsare-tsarensa."
"Bayan dogon nazari kan bukatar mai girma gwamna, majalisa ta amince masa ya naɗa hadimai 20."

Kara karanta wannan

Mambobin APC Sun Ɓarke da Zanga-Zangar Adawa da Sabon Kakakin Majalisa, Sun Faɗi Dalili

- Ismail Falgore.

Gwamnatin Tinubu Zata Fara Rabawa Daliban Najeriya Bashi

A wani rahoton na daban kuma Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatin zata fara taba wa ɗaliban rancen kuɗin da babu ruwa daga watan Satumba mai zuwa.

Babban Sakataren ma'aikatar ilimi, David Adejo, ne ya sanar da haka ranar Laraba yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida a birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262