Dan Majalisar LP Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Suka Zabi Tajudeen Abbas

Dan Majalisar LP Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Suka Zabi Tajudeen Abbas

  • Ɗan majalisar wakilai na jam'iyyar Labour Party (LP) ya bayyana dalilinsu na zaɓar ɗan takarar jam'iyyar APC a kujerar kakakin majalisa
  • Denis Agbo ya ce sun zaɓi Abbas Tajudeen ne bayan shirin da suka so su yi na zaɓar kakakin daga ɓangarensu bai yiwu ba
  • Ya ce ƴan majalisun jam'iyyun adawa sun so fitar da kakakin majalisa da mataimakinsa a tsakaninsu amma sai hakan bai yiwu ba

FCT, Abuja - Ɗan majalisar wakilai na jam'iyyar Labour Party (LP), Denis Agbo, ya kare dalilin da ya sanya takwarorinsa suka zaɓi ɗan takarar jam'iyyar APC, Tajudeen Abbas, a matsayin kakakin majalisar wakilai ta 10.

A zaɓen da aka gudanar wajen ƙaddamar da majalisar a ranar Talata, Abbas ya samu ƙuri'u 353 inda ya kayar da Idris Wase da Sani waɗanda suka samu ƙuri'u uku kowannen su.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Femi Gbajabiamila Ya Shirya Yin Murabus, Bayanai Sun Fito

Dalilin yan adawa na zabar Abbas Tajudeen
Abbas Tajudeen a lokacin rantsar da shi Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta ambato ɗan majalisar a yayin wata hira da gidan talbijin na Channels TV, yana cewa shirinsu na farko shi ne su marawa ƴan takara daga ɓangaren ƴan adawa baya, amma sai suka fasa yin hakan.

Sun yi ƙoƙarin samar da kakakin majalisar daga ɓangaren ƴan adawa

A kalamansa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Idan ka haɗa yawanmu muna da 183, 182 idan aka cire wanda ya rasu, mu ƴan ɓangaren adawa mu ne mu ke da rinjaƴe a majalisar."
"Akwai lokacin da mu ka yanke cewa masu yawa su nemi kujerun, amma PDP tafi yawan ƴan majalisa a ɓangaren marasa rinjaye inda take da 116, ƴan majalisun APC sun fi 170."
"Mun yanke hukuncin cewa da yawan da mu ke da shi, za mu iya samar da kakaki da mataimakinsa. An kai kujerar kakakin ɓangaren PDP, sai ta mataimaki ɓangaren LP. An kafa kwamitin mutum 11 domin tantancewa. Mun wuce wannan matakin."

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Gwamnonin APC, PDP Da Suka Halarci Zaben Shugabannin Majalisa Ta 10

"Mun ci gaba da shirye-shiryenmu, sai kuma kawai mu ka yanke cewa mu bari jam'iyya mai mulki ta samar da kakakin majalisa saboda suna da ƴan majalisu 177, fiye da na PDP."
"Kada ka manta a cikin mutum 182 ba kowa ba ne zai bayar da haɗin kai, abubuwa dai suka yi ta faruwa waɗanda suka sanya mu ka sake tunani."

Matam Abbas Sun Yi Abun Kunya a Zauren Majalisa

A wani labarin, kun ji yadda matan sabon kakakin majalisar wakilai suka yi ƙoƙarin dambace wa a zauren majalisar wakilai.

Matan na Abbas Tajudeen sun yi yunƙurin ba hammata iska ana tsaka da rantsar da shi saboda son tsayawa a kusa da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng