Matasa Sun Barke da Zanga-Zanga a Birnin Tarayya Abuja Kan Rikicin Majalisa

Matasa Sun Barke da Zanga-Zanga a Birnin Tarayya Abuja Kan Rikicin Majalisa

  • Wasu dandazon matasa sun fita gaban hedkwatar rundunar yan sanda ta ƙasa da ke Abuja, sun fara zanga-zanga ranar Laraba
  • A cewar shugabannin masu wannan zanga-zanga sun zabi yin haka ne domin nuna takaicinsu kan abinda ke faruwa a majalisar dokokin jihar Nasarawa
  • Sun kuma yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da shugaban yan sanda su sanya baki a rikicin shugabanci da ya raba majalisa gida biyu

FCT Abuja - Rahotanni sun nuna cewa wasu dandazon matasa sun fita zanga-zanga a gaban Hedkwatar rundunar 'yan sanda ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa matasan sun mamaye wurin ne domin nuna takaicinsu kan dambarwan shugabancin da ta ɓarke a majalisar dokokin jihar Nasarawa.

Matasa na zanga-zanga a Abuja.
Matasa Sun Barke da Zanga-Zanga a Birnin Tarayya Abuja Kan Rikicin Majalisa Hoto: thenationonlineng
Asali: UGC

Jagororin masu zanga-zangar sun bayyana cewa ba su ji daɗin rikicin shugabancin da a yanzu ya dabaibaye majalisar Nasarawa da ke shiyyar Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Abubuwa 11 da Suka Taimaki Tajudden Abbas Ya Zama Shugaban Majalisar Wakilai

Sun roƙi shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da Sufeta Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, su sa baki a wannan matsala da ta raba kan majalisar dokokin jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsu wannan shi ne lokacin da ya fi dacewa Tinubu da Sufeta Janar su gaggauta kai wa majalisa ɗauki tun kafin rikicin ya ƙara muni.

Daily Trust ta rahoto cewa matasan, waɗanda 'yan asalin jihar Nasarawa ne, sun toshe hanyar shiga hedkwatar yan sandan. Sun yi haka ne karkashin ƙungiyar masu kishin jihar Nasarawa.

Haka zalika matasan sun ɗaga allunan sanarwa ɗauke da rubutu daban-daban, suna zargin gwamna Abdullahi Sule, da yunkurin ta da yamutsi a jihar ta hanyar ƙaƙaba wanda yake so a majalisa.

Zanga-zanga kan rikicin Nasarawa.
Matasa Sun Barke da Zanga-Zanga a Birnin Tarayya Abuja Kan Rikicin Majalisa Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Yan sanda sun kwantar da hankalin masu zanga-zanga

Da yake yayyafa wa zuƙatan matasan ruwan sanyi, mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Kingsley Emeka, ya faɗa wa masu zanga-zangar cewa sakonsu zai isa kunnen IGP.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sa Labule da Sabon Shugaban Majalisar Dattawa, Gwamnoni 2 da Ganduje, Bayanai Sun Fito

Idan baku manta ba, dambarwa ta ɓalle a majalisar dokokin Nasarawa har ta kai ga zaɓen kakakin majalisa guda biyu, Honorabul Daniel Ogazi da Honorabul Balarabe Abdullahi.

Femi Gbajabiamila Ya Yi Murabus Daga Majalisar Wakilan Tarayya

A wani labarin na daban kuma Tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya yi murabus daga majalisa yau Laraba, 14 ga watan Yuni, 2023.

Hakan na kunshe a wasiƙar murabus da ya miƙa wa majalisar kuma sabon kakaki, Tajudeen Abbas, ya karanta a zaman ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262