Femi Gbajabiamila Ya Yi Murabus Daga Majalisar Wakilan Tarayya

Femi Gbajabiamila Ya Yi Murabus Daga Majalisar Wakilan Tarayya

  • Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Surelere 1, Femi Gbajabiamila, ya yi murabus daga majalisar wakilai ta ƙasa
  • Hakan na kunshe a wasiƙar murabus da ya miƙa wa majalisar kuma sabon kakaki, Tajudeen Abbas, ya karanta a zaman ranar Laraba
  • A halin yanzu, hukumar zabe ta kasa INEC ke da alhakin sake shirya zabe a mazaɓar domin cike gurbinsa

FCT Abuja - Tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya yi murabus daga majalisar wakilai domin maida hankali kan muƙaminsa na shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa.

Channels tv ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a wasiƙar murabus da gabatar a zauren majalisar kuma sabon kakakin majalisa, Tajudeen Abbas, ya karanta a zaman yau Laraba.

Tsohon kakakin majalisa ya yi murabus.
Femi Gbajabiamila Ya Yi Murabus Daga Majalisar Wakilan Tarayya Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoto a ɗazu cewa Gbajabiamila zai yi murabus daga majalisa, domin samun damar maida hankali kan aikin da ke gabansa a sabuwar gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda Matan Sabon Kakakin Majalisar Wakilai Suka Yi Abun Kunya a Zauren Majalisa, Bidiyo Ya Bayyana

Sai dai mutane sun fara guna guni bayan ganin tsohon kakakin ya yi rantsuwar kama aiki tare da sauran 'yan majalisar tarayya ranar Talata, 13 ga watan Yuni, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya haddasa ruɗanin cewa ta ya zai iya haɗa aikin majalisa da kuma aikin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa.

A halin yanzu, Gbajabiamila, mamba mai wakiltar mazaɓar Surulere 1 ya miƙa takardar murabus daga kujerar ɗan majalisar wakilan tarayya.

INEC zata shirya sabon zaɓe a mazaɓarsa

Wannan mataƙi zai bai wa hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) mai zaman kanta damar shirya sabon zaɓe domin mutanen mazaɓar su zaɓi wanda zai wakilce su a majalisa ta 10.

Tun a shekarar 2003, Gbajabiamila ke wakiltar mazabar Surulere 1 daga jihar Legas a ƙaramar majalisar tarayya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Haka nan ya sake lashe zabe karo na shida a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, ranar da INEC ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da yan majalisun tarayya.

Kara karanta wannan

Mambobin APC Sun Ɓarke da Zanga-Zangar Adawa da Sabon Kakakin Majalisa, Sun Faɗi Dalili

Majalisa Ta 10: Kar Ku Ga Laifina Idan Akpabio Ya Gaza, Sanata Ndume

A wani rahoton na daban kuma Ɗaya daga cikin jagororin kamfen Akpabio/Barau a majalisa ta 10, Sanata Ali Ndume, ya yi bayani mai jan hankali.

Sanata mai wakiltar Borno ta kudu, Ali Ndume, ya ce kar wanda ya ɗora masa laifi idan sabon shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya gaza yin abinda ake tsammani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262