Mambobin APC Sun Mamaye Zauren Majalisar Dokokin Jigawa Kan Zaben Kakaki

Mambobin APC Sun Mamaye Zauren Majalisar Dokokin Jigawa Kan Zaben Kakaki

  • Wasu mambobin jam'iyyar APC daga ƙaramar hukumar Jahun a Jigawa sun fita zanga-zangar adawa da zaɓen Idris Garba a matsayin sabon kakakin majalisa
  • Masu zanga-zangar sun nemi a bai wa wani daban matsayin maimakon Garba, wanda shi ne kakakin majalisar da ta gabata
  • Wannan ya biyo bayan matakin shugabannin APC na Jigawa, waɗanda suka yanke bai wa yankin Jigawa ta Kudu maso Yamna kujerar kakaki

Jigawa - Wasu mambobin jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Jahun ta jihar Jigawa sun fantsama kan tituna don nuna adawa da naɗa Idris Garba a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin jihar.

A rahoton da Channels tv ta haɗa, masu zanga-zangar, sun buƙaci a bai wa wanda bai taɓa rikewa ba mukamin maimakon Garba, tsohon kakaki a majalisar da ta gabata.

Zanga-zanga a majalisar dokokin Jigawa.
Mambobin APC Sun Mamaye Zauren Majalisar Dokokin Jigawa Kan Zaben Kakaki Hoto: channelstv
Asali: UGC

Meyasa mambobin APC suka tsunduma zanga-zanga?

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Gwamnonin APC, PDP Da Suka Halarci Zaben Shugabannin Majalisa Ta 10

Wannan ruɗani ya biyo baya ne sakamakon mataikin APC na miƙa kujerar kakakin majalisa zuwa shiyyar Jigawa ta Kudu maso yamma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan jam'iyyar APC ta sanar da ɗaukar wannan matakin, nan take aka tsayar da Idris Garba, tsohon kakakin da ya gabata domin ya ci gaba da jagorantar majalisar dokokin Jigawa.

Amma wani tsagin 'ya'yan APC daga ƙaramar hukumar Jahun sun sa kafa sun yi fatali da hakan wanda ya haddasa ɓarkewar zanga-zanga, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Su wa suka shirya wannan zanga-zanga?

Ƙungiyar matasan APC ta Arewa Maso Yamma reshen jihar Jigawa ce ta shirya zanga-zangar ta lumana wacce ta gudana ranar Talata, 13 ga watan Yuni, 2023.

Rahoto ya nuna cewa zanga-zangar ba iya zauren majalisar dokoki ta tsaya ba, mambobin sun gudanar da ita a gidan gwamnati da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Abubuwa 11 da Suka Taimaki Tajudden Abbas Ya Zama Shugaban Majalisar Wakilai

Sakataren ƙungiyar, Adamu Muhammad Na'Alla Jahun, a madadin masu zanga-zangar, ya ce sun yi haka ne domin jawo hankalin mambobin majalisa su farka daga bacci.

Ya ce burinsu su ƙara ankarar da 'yan majalisar kan bukatar zaɓen mutanen da ke da salo mai kyau da burin ciyar da jihar Jigawa gaba kuma waɗanda zasu haɗa kai da ɓangaren zartaswa don kawo ci gaba.

Katsina: An Zabi Nasir Daura a Matsayin Kakakin Majalisar Dokoki Ta 8

A wani labarin na daban kuma Nasir Daura mai wakiltar mazaɓar Daura, ya zama sabon kakakin majalisar dokokin jihar Katsina a wurin bikin rantsuwa ranar Talata.

Bayan haka majalisar ta zaɓi Runka a matsayin mataimakin kakaki da kuma Shamsuddeen Dabai a matsayin jagoran majalisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262