Femi Gbajabiamila Ya Shirya Yin Murabus, Bayanai Sun Fito
- Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya shirya yin murabus a matsayin ɗan majalisar wakilai
- Rahotanni sun tabbatar da cewa ɗan siyasar wanda ya fito daga jihar Legas zai miƙa takardar murabus ɗinsa a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni
- Hakan na nufin cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), za ta gudanar da sabon zaɓe domin cike gurbin da ya bari
FCT, Abuja - Tsohon kakakin majalisar wakilai kuma sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, zai miƙa takardar murabus ɗinsa a matsayin ɗan majalisa a yau Laraba a harabar majalisar wakilan.
Channels Television ta tabbatar da cewa tsohon kakakin majalisar zai yi murabus, domin ya samu ya mayar da hankali kan babban aikin da ke gabansa na shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin tarayya.
An yi ta nuna damuwa kan yadda zai iya haɗa ayyukan guda biyu ya gudanar da su, saboda tsohon kakakin an rantsar da shi a jiya Talata tare da sauran takwarorinsa, sannan har zaɓe ya yi na shugabancin majalisar.
INEC za ta gudanar da sabon zaɓe a Surulere 1
Sai dai, tabbataccen labarin da aka samu ya nuna ɗan majalisar mai wakiltar Surulere 1 zai miƙa takardar murabus ɗinsa, sannan hukumar shirya zaɓe ta INEC za ta gudanar da sabon zaɓe domin cike gurbin da ya bari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gbajabiamila ya kasance a majalisar wakilai tun shekarar 2003, sannan nasarar da ya samu a babban zaɓen 2023, ya sanya ya kasance karo na shida yana lashe zaɓen ɗan majalisar na Surulere 1.
Ya kasance ɗaya daga cikin ƴan majalisar wakilai da suka daɗe a majalisar a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.
Gbaja, kamar yadda magoya bayansa suke kiransa da shi, yana daga cikin manya-manyan ƴan siyasar jihar Legas, kuma abin koyi ga matasan ƴan siyasa masu taso wa.
Gwamnonin APC, PDP Da Suka Halarci Zaben Majalisa
A wani labarin, gwamnonin jam'iyyun APC da PDP sun halarci zaɓen shugabannin majalisa ta 10, da aka gudanar ranar Talata a birnin tarayya Abuja.
Gwamnonin sun je wajen zaɓen ne domin sanya idanu kan yadda zaɓen na shugabannin majalisa ya gudana.
Asali: Legit.ng