Katsina: An Zabi Nasir Daura a Matsayin Kakakin Majalisar Dokoki Ta 8
- Nasir Daura mai wakiltar mazaɓar Daura, ya zama sabon kakakin majalisar dokokin jihar Katsina a wurin bikin rantsuwa ranar Talata
- Bayan haka majalisar ta zaɓi Runka a matsayin mataimakin kakaki da kuma Shamsuddeen Dabai a matsayin jagoran majalisa
- An zaɓi sabbin shugabannin majalisar ne ta hanyar maslaha a wani zama da mai girma gwamna, Malam Dikko Raɗda, ranar Litinin
Katsina - Honorabul Nasir Daura, mamba mai wakiltar mazaɓar Daura, ranar Talata, ya zama sabon kakakkin majalisar dokokin jihar Katsina ta 8, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Magatakardan majalisar, Lawal Dansuleiman, ne ya rantsar da sabuwar majalisa ta 8 a madadin gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗda, ranar 13 ga watan Yuni.
Ya ce an zaɓi sabon shugaban majalisa ne ta hanyar masalaha a wurin ganawar gwamna Raɗda da masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi 34 wanda ya gudana ranar Litinin.
Sauran shugabannin Majalisa da aka zaɓa
Sauran kujerun shugabancin majalisar dokokin Katsina da aka zaɓa ta hanyar maslaha sun haɗa da Abduljalal Haruna Runka a matsayin mataimakin kakakin majalisa ta 8 da Honorabul Shamsuddeen Dabai a mataayin jagoran majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai kuma Honorabul Mustapha Yusuf Jibia a matsayin mataimakin jagoran majalisa, Honorabul Ibrahim Umar da kuma Salisu Rimaye a matsayin mai ladabtarwa da mataimakinsa bi da bi.
A wata sanarwa da aka jingina wa Raɗɗa, gwamnan ya ce ya ɗauki matakin maslaha ne da nufin ƙara danƙon haɗin kai da jan kowa a jiki yayin gudanar da ayyukan majalisa.
Sabon kakaki ya yi jawabin farko
A jawabinsa na godiya, sabon kakakin majalisar Katsina ya yaba wa abokan aikinsa bisa ganin ya dace kuma suka zaɓe shi a matsayin wanda zai jagorance su.
Ya kuma ɗauki alkawarin cewa zai ƙara yauƙaƙa kyakkyawar dangantar da ke tsakanin ɓangaren masu doka da kuma ɓangaren zartaswa.
Jim kaɗan bayan kammala rantsuwar kama aiki, Honorabul Nasir ya jagoranci sauran mambobin majalisar suka kai ziyara ta musamman ga gwamna Dikko Raɗɗa, Daily Post ta rahoto.
Hadimin midiya a gidan sabon jagoran majalisar Katsina, Shamsudeen Dabai, ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa ba wani zaɓe aka yi ba, masalaha aka cimma da mai girma gwamna.
Ɗan siyasan, AbdulHafiz Tukur Dabai, wanda ya halarci bikin rantsarwa ranar Talata, ya ce mai gidansu kakaki ya so nema amma gwamna ya kira su aka tattuna tun ranar Litinin.
Ya faɗa wa wakilinmu cewa:
"Muna kara gode wa Allah wanda ya bai wa mai gida wannan sabon matsayi kuma muna wa sabbin shugabannin majalisa addu'ar Allah ya basu ikon sauke nauyin da ya rataya a kansu."
"A zahirin gaskiya ba zaɓe aka yi ba, na san cewa burin mai gidana ya zama kakakin majalisa to amma gwamna Malam Dikko Radɗa ya kira su ranar Litini aka yi sulhu, aka ba shi jagoran majalisa."
"Kuma mai gida ya amince, ya rungumi kaddara cewa dama haka Allah ya tsara amma ba zamu hakura da kakaki ba, zamu tari gaba."
Bodinga, Dan Shekara 47 Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dokokin Sokoto
A wani rahoton na daban kuma Majalisar dokokin jihar Sakkwato ta zaɓi sabon shugaba da mataimakinsa ranar Talata.
Tukur Bala Bodinga, ɗan shekara 47 a duniya, mamba mai wakiltar mazabar Bodinga ne ya samu nasarar zama sabon shugaban majalisar dokokin.
Asali: Legit.ng