Matashi Mai Shekara 38 Ya Sake Zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara
- Majalisar dokokin jihar Kwara ta sake zaɓar matashi mai shekara 38 a duniya a matsayin saɓon wanda zai jagorance ta
- Engr. Yakubu Danladi-Salihu ya sake ɗarewa kan kujerar kakakin majalisar dokokin a karo na biyu bayan ya yi tazarce
- Majalisar dokokin ta 10 ta jihar Kwara ta samu ƴan majalisu mata da dama a cikinta ciki har da matashiyar ƴar majalisa mai shekara 26 a duniya
Jihar Kwara - Majalisar dokokin jihar Kwara ta sake zaɓar Engr. Yakubu Danladi-Salihu, a matsayin kakakin majalisar ta 10, rahoton Leadership ya tabbatar.
Danladi-Salihu, mai shekara 38 a duniya, yana wakiltar mazaɓar, Ilesa/Gwanara a ƙaramar hukumar Baruten ta jihar Kwara a majalisar.
An sake zaɓen Danladi-Salihu a matsayin kakakin majalisar karo na biyu bayan kuɗirin da Hon Halidu Danbaba ya gabatar wanda Hon Fatimah Arinola Lawal ta goya masa baya.
An kuma zaɓi Hon. Emmanuel Oyebode mai wakiltar mazaɓar Oke-Ogun a matsayin mataimakin kakakin majalisar ba tare da abokin hamayya ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Magatakardar majalisar dokokin, Hajia Jummai Kperogi, ita ce ta ƙaddamar da majalisar dokokin ta 10 a harabar majalisar da ke a birnin Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
An ƙaddamar da majalisar dokokin ne biyo bayan shelar da gwamnan jihar, Abdulrahman Abdulrazaq ya yi domin bin umarnin sashi 105(3) na kundin tsarin mulkin ƙasar nan na shekarar 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima.
Majalisar tana da ƴan majalisu mata
Sabuwar majalisar dokokin mai mambobi 24 tana da mata guda shida, ciki har da Rukayat Shittu mai shekara 26 a duniya da Hon AbdulRaheem Agboola, wacce aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP, cewar rahoton Daily Trust.
Ƴan majalisa takwas daga cikin ƴan majalisar dokokin ba wannan bane karonsu na farko a majalisar, yayin da ƴan majalisa 16 wannan ne karonsu na farko na zuwa majalisar.
Bilyaminu Moriki Ya Zama Sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara
Rahoto ya zo kan yadda majalisar dokokin jihar Zamfara ta zaɓi sabon shugabanta wanda zai ja ragamar majalisar.
Majalisar zaɓi Hon. Bilyaminu Ismail Moriki a matsayin sabon kakakinta ba tsre da abokin hamayya ba. Majalisar cike ta ke da ƴan jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng