Jerin Sunaye: Gwamna Obaseki Ya Rantaar da Sabbin Kwamishinoni 15 a Jihar Edo

Jerin Sunaye: Gwamna Obaseki Ya Rantaar da Sabbin Kwamishinoni 15 a Jihar Edo

  • Gwamnan jihar Edo ya rantsar da sabbin kwamishinoni 15 da ya naɗa a majalisar zartarwan gwamnatinsa ranar Talata
  • Obaseki, mamban jam'iyyar PDP ya buƙaci su zage dantse su ba da gudummuwa domin ciyar da jihar Edo gaba
  • Gwamnan ya ce tun zuwansa kan madafun iko, tawagarsa ta kawo ci gaba a jihar Edo wanda a yanzu kowa ke iya gani

Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ranar Talata, ya rantsar da sabbin kwamishinoni 15 a matsayin mambobin majalisar zartaswa na jihar.

Yayin wannan rantsuwar kama aiki da ya bai wa kwamishinonin, Obaseki ya buƙaci su zage dantse, su nuna juriya a kokarin gwamnatinsa na inganta rayuwar al'ummar jihar Edo.

Gwamna Obaseki tare da sabbin kwamishinoni.
Jerin Sunaye: Gwamna Obaseki Ya Rantaar da Sabbin Kwamishinoni 15 a Jihar Edo Hoto: Governor Godwin Obaseki
Asali: Facebook

Haka nan ya caji sabbin kwamishinonin da karsu yi ƙasa a guiwa a yunkurin bunƙasa tattalin arzikin jihar da kuma samar da walwala da jin daɗi ga talakawa.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamnan CBN: Tsohon Gwamna, Masu Bankuna Da Wasu Kwararru Da Ke Sa Ran Gaje Kujerar Emefiele

Jerin sunayen sabbin kwamishinoni 15 a Edo

Jaridar Punch ta kawo cikakkun sunayen sabbin kwamishinonin da gwamna ya rantsar a rahotonta, ga su kamar haka;

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Ethan Osaze Uzamere

2. Christopher Osaretin Nehikhare

3. Monday Osaigbovo

4. Dakta Joan Osa-Oviawe

5. Isoken Omo

6. Stephen Ehikhioya Idehenre

7. Oluwole Osaze-Uzzi

8. Patrick Uanseru

9. Dakta Samuel Alli

10. Adaze Aguele-Kalu

11. Kingsley Uwagbale

12. Uyi Oduwa Malaka

13. Joshua Omokhodion

14. Ojiefoh Enaholo Donatus

15. Christabel Omo Ekwu.

Jawabin gwamna Obaseki a wurin rantsar da kwamishinonin

Gwamnan ya bai wa sabbin mambobin majalisar zartarwan rantsuwar kama aiki ne a gidan gwamnatinsa da ke Benin City, babban birnin jihar Edo ranar Talata.

A jawabinsa, Obaseki ya tabbatar da cewa gwamnatinsa zata ƙara inganta tashar jirgin ruwan Benin, tashar Enterprise Park, da sauran manyan ayyuka domin habaka ayyukan masana'antu da bunƙasa tattalin arzikin Edo.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna APC Ba Shi Da Lafiya, Ya Miƙa Mulki Ga Mataimakinsa Ya Tafi Ƙasar Waje Ganin Likita

A rahoton Premium Times, Obaseki ya ce:

"Mun kafa nagartacciyar tawaga tun farkon wannan gwamnatin shekaru 6 da suka shige. Tawagar ta taimaka mana wajen cika manyan kudirorinmu na sauya akalar Edo zuwa inda ya dace."
"Ina ƙara gode wa mambobin majalisar zartarwa tsawon shekaru 6, waɗanda suka yi aiki tuƙuru wajen sake fasalin sabuwar Edo da muke gani a yau. Yanzu muna rantsar da tawagar da zata karkare komai."

Bodinga, Dan Shekara 47 Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dokokin Sokoto

A wani rahoton kuma Majalisar dokokin jihar Saƙkwato ta zabi mamba ɗan shekara 47 a matsayin sabon kakakin majalisa.

Da yake jawabi, ya ce a karkashin jagorancinsa majalisar dokoki zata tafi da kowane mamba kuma zata taimakawa gwamnatin Sakkwato.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262