Yanzu Yanzu: Lawan Ya Zama Kakakin Majalisar Borno Karo Na 4 a Jere
- Abdulkarim Lawan ya zama kakakin majalisar dokokin jihar Borno ta 10 a ranar Talata, 13 ga watan Yuni
- Wannan shine karo na hudu da Lawan ke darewa kan wannan kujera tun daga majalisa ta shida
- Haka kuma, Abdullahi Musa mai wakiltan mazabar Askira/Uba ya koma kan kujerarsa na mataimakin kakakin majalisar
Borno - Majalisar dokokin jihar Borno ta zabi Abdulkarim Lawan a matsayin kakakin majalisa ta 10, jaridar Leadership ta rahoto.
Hon. Lawan ya kasance kakakin majalisar dokokin majalisar ta tara kuma shi ke shugabantar majalisar tun daga ta shida.
Magatakardar majalisar, Mista Jidayi Mamza ya sanar da cewar majalisar ta samu izini daga Gwamna Babagana Zulum cewa ta gudanar da zamanta na farko a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, rahoton TVC.
Mamza ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Majalisar ta samu sako daga mai girma gwamnan jihar Borno Babagana Zulum inda ya bukaci ta gudanar da zamanta na farko a ranar Talata, 13 ga watan Yunin 2023."
Zababben dan majalisa mai wakiltan Marte, Gambomi Marte ya tsayar da Abdulkarim Lawan sannan zababben dan majalisa mai wakiltan Jere, Abba Kyari Kolo ya mara masa baya.
Majalisar ta kuma zabi tsohon mataimakin kakakin majalisar Abdullahi Musa daga mazabar Askira/Uba domin komawa kan kujerarsa ta mataimakin kakakin majalisa.
Lawan ya yi jawabin godiya
Su dukka yan majalisar sun amince da zabin sannan sun nuna shirinsu na aiki.
A jawabinsa na godiya jim kadan bayan ya karbi rantsuwar aiki, Hon. Abdulkarim Lawan, ya yaba ma yan majalisar kan zabarsa da suka yi, yana mai cewa kan gidan a hade yake.
Ya bukaci sabbin mambobin majalisar da aka rantsar da su sake zage damtse sannan su yi aiki kai da fata da bangaren zartarwa domin gyara jihar ta bangaren ilimi, tsaron abinci, tsaro da sauransu.
Kakakin majalisar ya kuma yi alkawarin kai majalisar zuwa mataki na gaba.
Kakakin majalisar ya kuma bayyana sunayen manyan jami'an majalisar da suka hada da shugaban majalisa, Dige Mohammed daga mazabar Kala Balge, babban mai tsawatarwa Baba Ali Modu daga mazabar Mafa, mataimakin shugaban majalisa, Malami Wakil Korede daga Damboa da Audu Mustapha daga Magumeri.
Hon Tajudeen Abass ya zama kakakin majalisar wakilai
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa Hon. Abbas Tajudeen ya zama kakakin majalisar wakilai.
Haka kuma, Hon. Benjamin Kalu, dan majalisa mai wakiltan mazabar Bende ta jihar Abia ya zama mataimakin kakakin majalisar wakilai.
Asali: Legit.ng