Akpabio Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki a Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa

Akpabio Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki a Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa

  • Sanata Godswill Akpabio ya karɓi shahadar kama aiki a matsayin shugaban majalisar Dattijan Najeriya ranar Talata, 13 ga watan Yuni
  • Sanatan, tsohon ministan Neja Delta ya kama aiki ne bayan doke babban abokin karawarsa, Abdul'aziz Yari daga jihar Zamfara
  • Akpabio, wanda ya samu goyon bayan shugaban ƙasa da APC mai mulki ya samu kuri'u 63 yayin da Yari ya tashi da ƙuri'a 46

FCT Abuja - Tsohon ministan Neja Delta kuma tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio, ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban majalisar dattawa.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an rantsar da Sanata Akpabio ne bayan ya samu nasarar lallasa abokin karawarsa, Sanata Abdul'aziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Akpabio Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki a Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa Hoto: SaharaReporters
Asali: Twitter

Akpabio ya samu kuri'u 63 a zaben da aka gudanar da safiyar Talata, 13 ga watan Yuni, 2023, yayin da Sanata Yari ya tashi da ƙuri'u 46.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jibrin Barau Daga Kano Ya Zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

Rahoton Channels tv ya tabbatar da cewa an kammala zaɓe da misalin karfe 9:15 yayin da Akpabio ya karɓi rantsuwar kama aiki da misalin ƙarfe 9:44 na safiyar Talata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabinsa, Sanata Akpabio, ya sha alwashin tafiyar da mulkin majalisar dattawa daidai da yadda kundin tsarin mulkin tarayya Najeriya ya tanada.

Takaitaccen tarihin siyasar Akpabio

Mista Akpabio, wanda lauya ne masanin dokokin kasa kuma babban ɗan siyasa ya riƙe muƙamin Ministan Neja Delta tsakanin 2019 zuwa 2022 karkashin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Sai dai ya yi murabus daga kujerar Minista a ranar 11 ga watan Mayu, 2022 bisa umarnin shugaban ƙasa na wancan lokacin Muhammadu Buhari domin shiga tseren neman tikitin takarar shugaban a inuwar APC.

Gabannin haka Sanata Akpabio, ya zauna a kujerar gwamnan jihar Akwa Ibom daga shekarar 2007 zuwa 2015 yayin da Abdul'aziz Yari ya zama gwamnan Zamfara a watan Afrilu, 2011, ya sauka a 2019.

Kara karanta wannan

Godswill Akpabio Ya Doke Abdulaziz Yari, Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

Akpabio/Barau: Abubuwan da Ya Dace a Sani Game da Sababbin Shugabannin Sanatoci

A wani rahoton kuma mun tattaro muku Abubuwan da ya dace ku sani game da aababbin shugabannin majalisar dattijai.

Legit.ng Hausa ta dauko maku tarihin Godswill Akpabio da kuma Barau Jibrin da su ka gaji Ahmad Lawan da Ovie Omo-Agege.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262