Yanzu-Yanzu: Jibrin Barau Daga Kano Ya Zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

Yanzu-Yanzu: Jibrin Barau Daga Kano Ya Zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

FCT, Abuja - Zababben sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Jibrin Barau, ya yi nasarar zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ba tare da hamayya ba.

Ya zama mataimakin ne bayan da tsohon gwamnan jihar Ebonyi kuma zababben sanata, David Umahi mai wakiltar Ebonyi ta Kudu ya zabe shi.

Zababben dan majalisa mai wakiltar Kwara ta Arewa, Salisu Mustapha, shima ya goyi bayan zaben Jibrin.

Barau ya amince da zabin da aka masa a matsayin Mataimakin Shugaban Majallisar Dattawa ta 10 ba tare da hamayya ba, The Punch ta rahoto.

Hakazalika, Legit.ng Hausa ta rahoto cewa an zabi tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa ta 10.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164