Shugaban Majalisar Dattawa: Hotuna Sun Bayyana Yayin da Akpabio, Uzodinma Suka Gana Da Tinubu a Villa
- Babban dan takarar kujerar shugaban majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio ya gana da shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin, 12 ga watan Yuni
- Taron ya kuma samu halartan Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo wanda aka zaba domin ya jagoranci kwamitin sasanta rikicin kujerar shugaban majalisar dattawan
- Bayan taron, Uzodimma ya nuna karfin gwiwar cewa dan takarar da APC ke so, Akpabio, shine zai yi nasara a matsayin shugaban majalisar dattawa na gaba
Kasa da awanni 24 kafin rantsar da majalisa ta 10, hugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin mai niyan zama shugaban majalisar dattawan Najeriya na gaba, Sanata Godwill Akpabio a fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 12 ga watan Yuni.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dattawa ke shirin zabar sabbin shugabanninta a ranar Talata, 13 ga watan Yuni.
Tinubu ya gana da Akpabio, Uzodimma, yan awanni kafin rantsar da majalisar dattawa ta 10
Wani mai amfani da Twitter Daddy D.O @DOlusegun, ne ya sanar da ci gaban a wata wallafa da ya yi a shafinsa inda ya hada da hotunan jiga-jigan kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A halin da ake ciki, Tinubu ya kafa wani kwamiti karkashin jagorancin shugaban kungiyar gwamnanonin APC kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, wanda shima ya hallara a yayin ganawar Akpabio da shugaban kasar a ranar Litinin.
Shugaban kasar ya yi wannan yunkurin ne don tabbatar da ganin cewa Godswill Akpabio ya dawo a matsayin shugaban majalisar.
Uzodinma ya tabbatar da hakan ne a cikin wata hira da manema labarai bayan ganawa da Tinubu a fadar shugaban kasa a ranar Litinin, Nigerian Tribune ta rahoto.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa kaso 90 na zababbun sanatocin suna goyon bayan tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom wanda ya ce shine zai yi nasara a takarar neman kujerar shugabancin majalisar.
Shugaban majalisar dattawa: Shettima ya yi gagarumin jan hankali ga zababbun sanatoci
A wani labarin kuma, mun ji cewa gabannin rantsar da zauren majalisa ta gaba, mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya bukaci zababbun sanatoci da su yi aiki da hankali wajen zabar shugabannin majalisar mai zuwa.
Da yake magana yayin zaman rufe majalisar dattawa ta tara a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni, Shettima ya fada ma yan majalisar cewa zaman lafiyan kasar ya fi cika aljihunsu daraja, jaridar The Cable ta rahoto.
Asali: Legit.ng