"Da Mun Hadu Zan Iya Marin Kwankwaso a Villa" Ganduje Ya Dau Zafi

"Da Mun Hadu Zan Iya Marin Kwankwaso a Villa" Ganduje Ya Dau Zafi

  • Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya kai ziyara fadar shugaban kasa a yau Juma'a, 9 ga watan Yuni
  • Ganduje ya ce da ace ya hadu da Sanata Rabiu Kwankwaso a Villa da zai iya marinsa
  • Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan aikin rusau da magajinsa Abba Kabir Yusuf yake yi

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa idan da ya hadu da magajinsa, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, a fadar shugaban kasa da ke Abuja da ya mare shi.

Mun dai ji cewa Kwankwaso ya gana da shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni, rahoton Daily Trust.

Kwankwaso da Ganduje
Yanzu-Yanzu: "Da Mun Hadu Zan Iya Marin Kwankwaso a Villa" Ganduje Ya Dau Zafi Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yayin da yake jawabi ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawa da Tinubu kan lamarin tsaro a jihar Kano bayan aikin rusau da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Ganduje ya nuna rashin gamsuwa da lamarin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu da Kwankwaso Sun Shiga Ganawa a Fadar Shugaban Kasa

"Na san yana gidan amma ba mu hadu ba. Amma da ace mun hadu, watakila da na mare shi."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ta rusau a Kano ba bisa ka'ida ba, Ganduje

Ganduje ya ce an gudanar da shirin rusau din ba tare da kowani bincike ko bayar da sanarwa daidai da dokar fili ba.

Tsohon gwamnan ya ce ya yi magana sosai kan lamarin yayin da yake kaiwa shugaban kasar rahoton lamarin kuma cewa ya aikewa Sufeto Janar na yan sanda, Usman Alkali Baba bayani kan lamarin da bidiyon sace-sacen da ya biyo bayan rusan.

Ya ce gwamnan wanda ya bayyana shi a matsayin karen farautar Kwankwaso baya jin dadi a yanzu saboda sukar da ya biyo bayan lamarin.

Tinubu ya gana da Kwankwaso a fadar Villa

Mun kawo a baya cewa shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawa da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso a Aso Rock, Abuja.

Kwankwaso na ɗaya daga cikin manyan 'yan takarar shugaban ƙasa na sahun gaba da suka kara da Tinubu a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng