Gwamnoni Sun Ziyarci Tinubu, Sun Bayyana Matsayarsu Kan Batun Cire Tallafin Man Fetur
- Gwamnonin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga matakin da Shugaba Tinubu ya ɗauka na kawo ƙarshen biyan tallafin man fetur
- Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), ta taya Shugaba Tinubu murna kan yadda ya dakatar da tallafin man fetur tare da yin alƙawarin haɗa kai da shi don daƙile tasirin da ke tattare da hakan
- Shugaba Tinubu ya yi kira ga manyan 'yan siyasa da su haɗa kai wajen yaƙar talauci tare da jaddada bukatar ajiye siyasar ɓangaranci domin ci gaban Najeriya da gina ƙasa
Abuja - A ranar Laraba, 7 ga watan Yuni ne gwamnonin Najeriya suka bayyana goyon bayansu ga cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi.
Gwamnonin, ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya sun nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasar a taronsu na farko da suka yi da shi a Abuja, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Gwamnoni sun taya Tinubu murna kan matakan da ya ɗauka
Gwamnonin waɗanda gwamnan jihar Kwara kuma shugaban gwamnonin Najeriya, AbdulRahman AbdulRazaq ya jagoranta, sun nuna farin cikinsu dangane da batun cire tallafin, batun gwamnatin haɗaka, da kuma iya ƙwarewar Tinubu a shugabanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun kuma taya Shugaba Tinubu murna kan yadda ya magance matsalar tallafin man fetur, inda suka yi alƙawarin yin aiki tare da shi don magance ɗan gajeren tasirin da hakan zai haifar.
Tinubu ya nemi haɗin kan gwamnoni
A baya dai Shugaba Tinubu ya yi kira ga gwamnonin da su haɗa kai da Gwamnatin Tarayya wajen shawo kan matsalar talauci da ya yi wa ƙasa katutu, inda ya ce bai kamata a ci gaba da tafiya a haka ba.
A rahoton Leadership, Tinubu ya kuma shawarci manyan 'yan siyasa da su yi watsi da bambance-bambancen da ke tsakaninsu tare da mai da hankali wajen rage wahalhalu da raɗaɗin da jama’a ke ciki.
A cewarsa:
“Muna iya ganin illar talauci a fuskokin mutanenmu. Talauci ba gadonsa ake ba, daga cikin al’umma ne. Burinmu shi ne mu kawar da talauci. A ajiye siyasar bangaranci gefe guda, mun zo ne domin Najeriya, domin mu gina ƙasa’’.
Tinubu ya gana da 'yan kasuwar man fetur
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Tinubu ya gana da manyan 'yan kasuwar man fetur, dangane da batun cire tallafin man, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ganawar dai na zuwa ne a lokacin da jama'a da dama ke nuna adawa da cire tallafin man da aka yi, gami da hauhawar farashinsa.
Asali: Legit.ng