Cire Tallafin Mai: Gwannan Kaduna Ya Shiga Ganawa da Shugabannin Kwadugo

Cire Tallafin Mai: Gwannan Kaduna Ya Shiga Ganawa da Shugabannin Kwadugo

  • Gwamnan Kaduna, Malam auga Sani, ya gana da wakilan ƙungiyoyin kwadugo ƙan batutuwan da suka shafi cire tallafin mai
  • Ƙungiyoyin kwadugo karkashin NLC sun fara shirye-shiryen shiga yajin aiki kan matakin gwamnatin tarayya na kara farashin fetur
  • Sai dai a wata sanarwa, gwamnatin Ƙaduna ta ce tsaron zai duba hanyoyin magance ƙuncin da takalawa ka iya tsintar kansu a ciki

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya sa labule da shugabannin ƙungiyoyin kwadugo reshen jihar kan shirinsu na shiga yajin aiki.

The Nation ta tattaro cewa ƙungiyar kwadugo ta ƙasa (NLC) ta shirya tsunduma yajin aiki a faɗin Najeriya kan matakin gwamnatin tarayya na cire tallafin man Fetur.

Uba Sani.
Cire Tallafin Mai: Gwannan Kaduna Ya Shiga Ganawa da Shugabannin Kwadugo Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Ana tsammanin a wurin ganawar Malam Sani da jagororin NLC, za su kafa kwamitoci biyu da zasu zauna su yi nazarin hanyoyin warware rikicin da aka iya biyo bayan sakamakon cire tallafin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Labule Da Kungiyar Ma'aikata Ta Kasa Kan Cire Tallafin Man Fetur, Bayanai Sun Fito

Shugabannin ƙungiyoyin kwadugon sun shiga gana wa da mai girma gwamna bisa jagorancin shugaban NLC na Kaduna, Kwamaret Ayuba Magaji Suleiman.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnatin Kaduna ta yi karin bayani

Gwamnatin jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ta tabbatar da ganawar Uba Sani da shugabannin kwadugo a wani rubutu da ta wallafa a shafin Tuwita.

Ta ce mai girma gwamma ya kira taron ne domin lalubo hanyar da za'a bi don magance wahalhalun da mutanen Ƙaduna ka iya shiga biyo bayan cire tallafin man Fetur.

"Mai girma gwamna, Malam Uba Sani, ya gana da wakilan ƙungiyoyin kwadugo a jihar Kaduna kan batun cire tallafin man Fetur da kuma lalubo hanyar magance wahalhalun da lamarin ka iya jefa mutanen jihar."

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa wannan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta zauna da kungiyoyin a matakin ƙasa duk a kokarin shawo kansu kar su shiga yajin aiki.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PGF Sun Ɗauki Matsaya Kan Batun Cire Tallafin Man Fetur a Najeriya

'Yan Daba Sun Lakaɗa Wa Ɗan Takarar Gwanan PDP Dukan Tsiya a Kotu

A wani labarin kuma Wasu tsagerun yan daba sun lakaɗa wa tsohon ɗan takarar gwamna a inuwar PDP dukan tsiya a kusa da Kotu a jihar Ogun.

Rahoto ya nuna 'yan daban sun yi cincirindo a kusa da kotun yayin fara zaman sauraron karar zaben gwamnan Ogun.

Bayan abinda suka yi wa ɗan siyasan a gaban jami'an tsaro, yan daban sun kara wata ta'asar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262