Yan Daba Sun Farmaki Ayarin Gwamna Yahaya Bello Na Jihar Kogi
- Wasu gungun mutane da ake zaton 'yan daba ne sun farmaki ayarin gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ranar Asabar da tsakar rana
- Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya ce 'yan daban sun tare ayarin gwamna a hanyar zuwa Lokoja daga Abuja
- A halin yanzun jami'an tsaro sun baza komarsu domin cafko duk mai hannu a harin a doka ta hukunta shi
Kogi - Wasu miyagu da ake kyautata zaton 'yan daba ne sun farmaki ayarin gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, yayin da yake hanyar komawa Lokoja daga birnin tarayya Abuja.
Tribune ta tattaro cewa hakan na kunshe a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya raba wa 'yan jarida ranar Asabar.
Ya ce wasu mutane da ake tsammanin magoya bayan Alhaji Muritala Yakubu Ajaka ne suka tare mai girma gwamna kana suka farmake shi da misalin karfe 12:30 na tsakar rana yau Asabar.
Sanarwan ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Lamarin ya faru a kusa da sansanin sojin ruwa, kilomita kaɗan gabanin isa Lokoja kuma a wurin aka hangi ayarin Muritala Yakubu Ajaka, wanda daga ganin gwamna na zuwa suka tsohe hanyar."
"Daga nan sai wasu 'yan daba ɗauke da bindigogi suka buɗe wa ayarin mai girma gwamna wuta. Wasu daga cikin jami'an tsaro da hadiman da ke tare da ayarin gwamna sun ji raunuka."
"Tuni aka garzaya da waɗanda suka rauni Asibiti domin kula da lafiyarsu. Muna kira ga ɗaukacin mutanen Kogi su kwantar da hankulansu yayin da jami'an tsaro suka bazama don kamo masu hannu a harin."
Haka nan kwamsihinan ya tabbatar da cewa mai girma gwamna ya tsira ba abinda ya same shi daga harin kuma gwamnatin Kogi zata tabbatar da komai ya koma kan doka da oda.
"Gwamnati zata tabbatar da doka da oda kuma duk mai hannu a harin zai girbi abinda ya shuka. Mai girma gwamna ya gargaɗi mambobin APC kar su kuskura su nemi kai harin ɗaukar fansa."
Matawalle Ya Siyo Motocin N2.79bn Amma Bai Bar Ko Daya Ba, Gwamnan Zamfara
A wani labarin kuma Gwamna Lawal na jihar Zamfara ya gano makudan kuɗin da Matawalle ya kwashe ya siyo motoci amma babu ko ɗaya bayan ya bar mulki.
Gwamnan ya ce Matawalle ya ba da kwangilar siyo motocin da za'a raba wa manyan jami'an gwamnati a ma'aikatu, sashi-sahi da hukumomin na kimanin N1,149,800,000.
Asali: Legit.ng