Bola Tinubu: Shugaban Kasa Na Iya Sako Yan Chanji a Gaba Idan Ya Yi Nasara Kan Cire Tallafin Mai

Bola Tinubu: Shugaban Kasa Na Iya Sako Yan Chanji a Gaba Idan Ya Yi Nasara Kan Cire Tallafin Mai

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya fara cika aiki a ranar Litinin daga jawabin rantsar da shi kamar yadda ya daukarwa yan Najeriya alkawari yayin kamfen dinsa
  • Yan kasuwar mai sun fara yakarsa tun kafin ya bar kan mumbari a ranar Litinin bayan ya sanar da cire tallafin mai, sun rufe gidajen mai da dama sannan suka kara farashin man
  • Sai dai kuma, idan Tinubu ya yi nasarar cire tallafin mai, yan chanji na iya zama manyan yan Najeriya na gaba da za su yake shi

Shugaban kasa Bola Tinubu ya tsaya tsayin daka kan maganarsa na cika aiki tun daga jawabinsa na farko bayan rantsar da shi kamar yadda ya yi alkawari yayin yakin neman zabensa.

Gwamnatocin baya sun sha yin magana kan barazana da hatsarin tallafin mai ga tattalin arzikin Najeriya amma sun gaza cire shi yayin da yan kasuwa ke saurin kara farashin man fetur da kuma sawa ya yi karanci a kasuwa, wanda galibi yake sa yan kasa yin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu Na Shirin Rage Alawus Din Yan Bautar Kasa? Gaskiya Ta Bayyana

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
Bola Tinubu: Shugaban Kasa Na Iya Sako Yan Chanji a Gaba Idan Ya Yi Nasara Kan Cire Tallafin Mai Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Sai dai kuma, da alama gwamnatin Tinubu ta daura damarar cire tallafin man fetur din da tabbatar da ganin cewa bai sake bayyana a tattalin arzikin Najeriya ba da yanayin yadda take gudanar da harkokinta.

Saboda haka, idan Tinubu ya yi nasara a yakinsa da tallafin mai, abu na gaba da sabuwar gwamnatin za ta iya sanyawa a gaba ita ce 'Kasuwar chanji', wani tsari da yan tsirarun mutane ke amfana da shi da kuma yin illa ga farashin chanjin kudin kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Harkar canji yana kunshe da manyan yan Najeriya wadanda ke siyar da dala a 'kasuwar bayan fage'.

Wadannan mutane na samun dala masu yawan gaske daga babban bankin Najeriya (CBN), ta hanyar amfani da sanayya da kamun kafa sannan su sake siyar da su da tsada a kasuwar bayan fage.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya su Shirya, NNPC Ya Kara Farashin Man Fetur a Duk Gidajen Mai da Ke Karkashinsa

A ranar Laraba, 31 ga watan Mayu, farashin chanji a hukumance ya kasance N461 kan kowace dala yayin ake siyar da shi kan N745 a kasuwar bayan fage.

Dalilin da zai sa Tinubu ya yaki yan chanji

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a gidan gwamnati a ranar Talata, 30 ga watan Mayu, wacce ta kasance ranarsa ta farko a ofis, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bayyana cewa sun nuna turjiya sosai a kan sabuwar manufar amma sabuwar gwamnatin tana da niyan karya shi.

A cewar Shettima, dole tallafin man fetur ya tafi sannan dole ninkanya a farashin chanji ya tsaya. Ya kara da cewar idan Najeriya bata kawo karshen tallafin ba, tallafin zai kawo karshen Najeriya.

Shin Tinubu zai yaki tallafi da yan chanji?

Lokaci ne zai nuna ko Tinubu zai yi nasara a yaki da ya daukarwa kansa da gwamnatinsa.

Hakan ya kasance ne saboda tsarin chanjin kudin kasar ya dade kamar dai tallafin, idan ma bai fi shi tsufa ba, kuma ya zama ruwan dare da yaki da shi zai zama kamar raba wasu mutane da hanyar cin abincinsu a kasar.

Kara karanta wannan

Tinubu: Muhimman Abubuwa 7 da Aka Tsakura Daga Jawabin Sabon Shugaban Kasa

Babban bankin Najeriya ya karya darajar Naira

A wani labarin, mun ji cewa babban bankin CBN ya karya darajar Naira a kan Dala inda aka saida kudin Amurkan a kan N631 a maimakon N461.

An tattaro cewa masu shigo da kaya daga kasashen waje sun saye Dala ne jiya a kan N631.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: