Abin Da Buhari Ya Gaza Yi A Shekarunsa 8 Kan Mulki, Mataimakin Shugaban APC Ya Yi Bayani

Abin Da Buhari Ya Gaza Yi A Shekarunsa 8 Kan Mulki, Mataimakin Shugaban APC Ya Yi Bayani

  • Kwanaki kaɗan da miƙa mulki ga shugaba Tinubu, gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ta tsawon shekaru 8 ta sha suka a wurin wasu
  • Mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Salihu Mohammed Lukman ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta ki daukar matakan tunkarar manyan ƙalubalen da suka addabi ƙasa a lokacin
  • A cewar Lukman, hakan ne ya janyo matsaloli da kuma gazawar gwamnatin da Buhari da Osinbajo suka jagoranta

Abuja - Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa na yankin Arewa maso Yamma, Salihu Mohammed Lukman ya ba da bayanin yadda aka tafiyar da gwamnatin Buhari da ta gabata.

A cewar Lukman, a shekaru takwas da gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ta yi, ba ta ɗauki matakan tunkarar ƙalubalen da ya addabi ƙasar a lokacin ba.

Abinda Buhari ya gaza aiwatarwa a shekarunsa na Mulki
Lukman ya ce Buhari ya gaza daukar matakan dakile matsalolin da suka addabi kasa a lokacin mulkinsa. Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Abin da Buhari da APC suka kasa yi, Lukman ya yi bayani

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wakilan Amurka, Birtaniya Da Saudiyya, Ya Yi Wani Muhimmin Alkawari

Jigon na APC ya kuma ce jam’iyyar mai mulki ta gagara cika alƙawuran da ta yi wa ‘yan Najeriya a lokacin yaƙin neman zaɓe, saboda ta gaza amfani da nasarar zaɓenta yadda ya kamata, in ji rahoton Daily Trust.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lukman a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 31 ga watan Mayu a Abuja, ya ce ɗaya daga cikin gazawar gwamnatin APC tun bayan lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2015, shi ne barin da dama daga cikin jami’an da gwamnatin PDP ta naɗa domin su ci gaba da yi wa Gwamnatin Tarayya hidima.

Lukman, wanda kuma mamba ne a kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na kasa (NWC) ya ce:

“Idan har za a faɗi gaskiya, a matsayinmu na jam’iyya, ba mu yi amfani da nasarar zaɓenmu yadda ya kamata ba. Tun a shekarar 2015, bayan mun ci zaɓen shugaban ƙasa, mun bar wasu da dama daga cikin waɗanda PDP ta naɗa muƙamai kan su ci-gaba da yin aiki da gwamnatin tarayya, ciki kuwa har da Mista Godwin Emefiele da ya gada a matsayin gwamnan CBN.”

Kara karanta wannan

Rantsar Da Tinubu: Datti Baba-Ahmed Ya Dau Zafi, Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya

Lukman ya ce barin irin waɗannan mutanen ya janyowa gwamnatin APC gaza cimma manufofinta da ta yi amfani da su lokacin yaƙin neman zaɓe.

Haka nan kuma akwai batun barin waɗanda basu yi wani abun kirki ba su ci-gaba da riƙe muƙamansu.

Abinda ya hana Buhari yin jawabi a bikin rantsarwar 2019

A labarinmu na baya, kun karanta dalilin da ya sanya tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ƙin yin jawabin karɓar mulki a lokacin da aka rantsar da shi karo na biyu a 2019.

Jama'a da dama, musamman ma dai 'yan jam'iyyun adawa sun caccaki Buharin, inda suka bayyana cewa rashin ɗaukar 'yan ƙasa da muhimmanci ne ya hana shi yin jawabi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng